'Babba ne Sosai,' An Fadi Wani da Haɗarin Jirgin NNPCL Ya Ritsa da Shi
- An fara samun bayanai kan mutanen da suka yi haɗari a wani jirgin sama da ya fado kasa a cikin ruwa a wani yanki na Kalaba
- A halin yanzu, an fitar da sunan matukin jirgin wanda an ce ya shafe shekaru sama da 20 yana aiki kuma yana rike da babban muƙami
- Kamfanin mai na NNPCL ya bayyana cewa jirgin da ya fadi a Kalaba ya dauko jami'ansa ne zuwa wajen wani aiki na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar matukan jirgin sama ta kasa (NAAPE) ta yi bayani kan hadarin jirgin da aka yi a Kalaba a ranar Alhamis.
NAAPE ta bayyana cewa babban matukin jirgin kwararre ne kuma yana da gogewar aiki na shekaru sama da 20.
Jaridar Business Day ta wallafa cewa matuƙa biyu ne a cikin jirgin yayin da ya fado kasa kuma Yakubu Dukas ne ke jagorantar tafiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban matukin jirgi da ya yi hadari
Kungiyar NAAPE ta bayyana cewa Yakubu Dukas ne babban matukin jirgin, kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar matuka jirgin sama ta kasa.
Tribune ta wallafa cewa NAAPE ta kara da cewa Yakubu Dukas yana da gogewa a kan tukin jirgin sama, ya shafe shekaru sama da 20 a harkar.
Zuwa yanzu ba a fitar da sanarwa ko Yakubu Dukas ya rasu ba, kuma ana jiran bayanai daga hukumomi kan halin da ake ciki.
NAAPE ta yi kira ga gwamnati
Kungiyar matuƙa jirgin sama ta kasa ta yi kira ga gwamnati kan tabbatar da yin bincike domin gano dalilan haɗuran jirgi a Najeriya.
NAAPE ta ce bayan bincike, akwai buƙatar a tabbatar da an dauki matakin da ya dace domin hana faruwar haɗuran jirgin sama a kasar nan.
A karshe kungiyar NAAPE ta ce tana tare da iyalan dukkan wadanda hadarin jirgin ya ritsa da su cikin jimami kuma tana musu addu'a.
Tinubu ya yi jaje kan haɗarin jirgin NNPCL
A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin saman Turkiyya ya yi saukar gaggawa a filin jirgin JFK da ke birnin New York da matukin jirgin ya mutu ana tsakiyar tafiya.
Jirgin ya taso ne daga Seattle da zummar sauka a Istanbul lokacin da abin ya faru, kamar yadda kamfanin ya fitar da sanarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng