An Yi Watsi da Albashin N70,000, an Bukaci NLC Ta Tursasawa Tinubu Biyan N250,000

An Yi Watsi da Albashin N70,000, an Bukaci NLC Ta Tursasawa Tinubu Biyan N250,000

  • Kungiyar yan fansho a Kudancin Najeriya ta yi watsi da maganar ƙarin albashi zuwa N70,000 da gwamnatin tarayya ta yi
  • Kungiyar ta ce mafi ƙarancin albashin ba zai tabuka komai ba lura da yadda ake tsadar rayuwa da kuma karin kudin man fetur
  • Legit ta tattauna da wani ma'aikaci, Ali Babayo kan jin halin da yake ciki a kan kudin da yake kashewa a kowane wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti - Ƙungiyar yan fansho a Kudu maso Yammacin Najeriya ta yi Allah wadai da karin albashin N70,000 da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Yan fanshon sun ce gwamnatin tarayya ta yi wa yan kwadago wayo da suka karbi kudi N70,000 a halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fadi yadda aka yi gumurzu wajen yunkurin kama Yahaya Bello

Yan kwadago
Yan fansho sun bukaci karin albashi zuwa N250,000. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa yan fanshon sun bukaci kungiyar kwadago ta koma teburin sulhu da gwamnatin tarayya kan karin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan fansho sun yi watsi da N70,000

Kungiyar yan fansho a Kudu maso Yammacin Najeriya (NUP) ta yi watsi da karin albashin ma'aikata zuwa N70,000 da yan kwadago suka yarda yayin tattaunawa da gwamanti.

Kungiyar NUP ta ce ko da gwamnatin tarayya ta fara biyan kuɗin ba zai tsinana abin kirki ga ma'aikata ba lura da yadda aka shiga tsadar rayuwa.

Yan fanshon sun ce kungiyar kwadago ba ta nuna dabara ba yayin tattaunawa da gwamnatin kan mafi ƙarancin albashi kwata kwata.

Yan fansho sun buƙaci albashin akalla N250,000

Kakakin kungiyar NUP, Dakta Olusegun Abatan ya ce dole a sake zama kan albashi tun da gwamnatin tarayya ta kara kudin fetur.

Kara karanta wannan

'Ya so biya mana kudin jirgi,' Yan kwadago sun tono sirrin zamansu da Tinubu

Punch ta wallafa cewa Dakta Olusegun Abata ya ce yan kwadago su koma wajen gwamnatin tarayya su jajirce a dawo da mafi ƙarancin albashi N250,000.

Har ila yau yan fanshon sun koka kan yadda yan siyasa suke fantamawa da kudin kasa amma suna kira ga talakawa su kara hakuri.

Legit ta tattauna da Ali Babayo

Wani ma'aikacin gwamnati a jihar Gombe, Ali Babayo ya ce maganar da yan fansho suka yi tana kan hanya.

Ali Babayo ya ce albashin da ake biyansa ko mako bai yi zai kare saboda haka ya ce akwai bukatar a kara albashi sama da N70,000.

Za a kara albashi a jihar Ebonyi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Ebonyi ta sanar da cewa shirye shiryen fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi sun kusa kammaluwa a jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar Ebonyi, Jude Okpor ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng