An Gano Bidiyon Bello Turji Yana Shan Alwashi Bayan Kwace Motocin Sulken Sojoji

An Gano Bidiyon Bello Turji Yana Shan Alwashi Bayan Kwace Motocin Sulken Sojoji

  • An gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulke na sojoji guda biyu a daji
  • Yan ta'addan daga bisani sun kwashe makaman da ke cikin motocin tare da banka musu wuta a jihar Zamfara
  • Hakan ya biyo bayan makalewar motocin sojojin a cikin tabo yayin da suka yi kokarin kai hari kan 'yan bindigan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - An yada wani faifan bidiyo mai tayar da hankali da 'yan ta'adda ke bankawa motocin sulke na sojoji wuta.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mata sun zargi rundunar sojojin kasa, sun nemi a janye dakaru daga yankin Ibo

Bello Turji ya kona motocin sojoji na sulke a jihar Zamfara
Sojoji sun bar motocin sulkensu da suka makale a tabo inda Bello Turji ya kona su. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Zamfara: Bello Turji ya kona motocin sojoji

A cikin faifan bidiyo da @shehu_mahdi ya wallafa, an gano yadda yan bindiga ke kwasar kayan da ke cikin motocin kafin kona su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne bayan sojoji sun janye daga kai harin da suka yi niyya saboda wasu matsaloli.

Motar sojojin ta makale ne a cikin tabo inda suka sake kawo wata domin cire ta daga ciki amma abin ya ci tura.

Yan ta'adda sun kwashe makaman sojoji

Daga bisani yan bindiga sun iso wurin inda aka yi ta kai ruwa rana amma ba a samu rasa rai ba kamar yadda aka tabbatar.

Daga karshe, sojojin sun yanke shawarar barin motocin sulken a wurin inda yan bindigan suka iso tare da kwashe dukan abin da ke ciki.

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Yan bindigan sun kwashe alburusai da makamai a cikin motocin kafin su banka musu wuta yayin da Bello Turji da yaransa ke murna da shewa.

Sokoto: An cafke yaran Bello Turji

A wani labarin, kun ji cewa Jami'an tsaro sun yi nasarar kama wasu rikakkun yan bindiga a jihar Sokoto da ke Arewacin kasar.

Daga cikin wadanda aka kaman sun hada da na hannun daman kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji da ya addabi al'umma.

Jami'an tsaron sun yi nasarar cafke miyagun ne a wani samame da suka gudanar a kokarin dakile yan bindiga a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.