NAFDAC Ta Bukaci ’Yan Najeriya Su Kauracewa Cin Burodi? Sabon Bayani Ya Fito
- Hukumar NAFDAC ta fito ta yi karin haske kan rahoton da ke yawo a kafofin sada zumunta cewar ta hana 'yan Najeriya cin burodi
- NAFDAC ta ce ko kadan ba ta shawarci 'yan Najeriya a kan kauracewa burodi da ake sarrafawa a kasar ba saboda saccharine
- Sai dai kuma hukumar ta ce amfani da sinadarin saccharine da wasu masu sarrafa burodi ke yi ya sabawa ka'idojin NIS da GSFA
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta yi magana kan rahoton da ke yawo na cewa ta gargadi 'yan Najeriya daga cin burodi.
Shugabar NAFDAC, Moji Adeyeye, ta ce hukumar ba ta shawarci ‘yan Najeriya da kada su ci biredi ba, sabanin rahoton da ake yadawa a intanet.
NAFDAC ta hana cin burodi?
A wata sanarwa da NAFDAC ta fitar a shafinta na X, Adeyeye ta bayyana cewa bidiyo da ake yadawa, wanda ke ikirarin cewa hukumar ta hana a ci burodi ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Bidiyon da ke nuna cewa hukumar NAFDAC ta shawarci ‘yan Najeriya da su guji burodi saboda amfani da sinadarin saccharin ba haka ba ne.
"Bidiyon bai nuna ainihin abin da hukumar NAFDAC ta tattauna kansu a taron masu ruwa da tsaki a ranar 16 ga Agusta, 2024, a Ibadan, jihar Oyo ba."
- A cewar shugabar NAFDAC.
Amfani da saccharine a burodi
Sai dai Adeyeye ta fayyace cewa amfani da sinadarin saccharine a cikin burodi ya sabawa ka'idojin masana'antu na Najeriya (NIS) da ka'idojin amfani da sinadare a abinci na GSFA.
Hukumar NAFDAC ta jadda matsayarta kan amfani da sinadarin saccharine, inda shugabar ta ce:
"Duk wani mai sarrafa burodi da aka samu ya na amfani da sinadaran da ba a yarda da su ba kamar saccharine zai fuskanci hukunci.
"Hukumar ta jaddada cewa ko kadan ba ta shawarci 'yan Najeriya da su guji burodi da ake sarrafawa a kasar ba."
Hukumar ta kuma nesanta kanta daga bidiyon da ake yadawa tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da kare 'yan Najeriya daga duk wani abinci ko sha mai illa ga lafiya.
Burodi ya kusa kai fetur tsada
A wani labarin, mun ruwaito cewa karancin burodi da ake samu a wasu jihohin Arewacin kasar nan ya sanyawa farashinsa tashin gwauron zabi.
Ana ganin burodin ya yi tsada ne saboda tsadar fulawa, inda aka ce buhun fulawa da a baya ake sayar da shi kan N53,000 zuwa N55,000, yanzu ya koma N67,000 zuwa N70,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng