Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar

Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar

- Kungiyar masu gidajen burodi ta Nigeria, AMBCN, ta sanar karin farashin burodi da sauran kayayaki kamar biskit da kashi 30 cikin 100

- Kungiyar, ta bakin shugabanta na kasa Mansur Umar ta ce karin ya zama dole ne duba da yadda flawa da sauran kayan hada burodi suka yi tsada

- Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Nigeria ta taimaka domin ganin an rage farashin kayayyaki musamman flawa

Kungiyar masu gidajen burodi ta Nigeria, AMBCN, ta umurci mambobinta a dukkan sassan kasar su kara farashin burodi, biskit da sauran kayayyakin da kashi 30 cikin 100 saboda mummunan halin da tattalin arzikin kasar ta shiga, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta yi bayanin cewa ta yi karin farashin ne sakamakon karuwar farashin kayayyakin hada burodi kamar sukari, bota, flawa, yist da sauransu.

Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar
Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar. @TheNationNews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

Wannan umurnin na daga cikin matakan da aka cimma a karshen taron shugabannin kungiyar da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban kungiyar na kasa, Mansur Umar, ya yi bayanin cewa: "Bayan la'akari da tashin gauron zabi da kayayakin hada burodi suka yi, domin tabbatar da cewa sana'ar mu bata durkushe ba, kungiyar ta yanke shawarar kara kudi da kashi 30 cikin 100."

Kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta bisa karin farashin da ta ce yana tilasta wasu mambobinta dena sana'ar.

KU KARANTA: An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau

Yayin da ta ke kira ga mambobinta su kara farashi da kashi 30 domin tsadar kayayyakin aikinsu, AMBCN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakan ganin an rage tsadar flawa da ke yi wa sana'arsu illa.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel