Burodi Ya Kusa Kai Fetur Tsada a Wasu Jihohin Arewa, Masu Tsaraba Sun Koka

Burodi Ya Kusa Kai Fetur Tsada a Wasu Jihohin Arewa, Masu Tsaraba Sun Koka

  • Ana tsaka da fama da karancin man fetur a kasar nan ne kuma sai aka fara samun tsadar burodi da karancinsa a wasu jihohin Arewa
  • Bincike ya gano cewa yanzu haka jihohin Kano da Kaduna da Katsina na fama da tashin farashin burodi, kuma an rage buga shi
  • Wasu masu tsaraba da burodi a Kano sun bayyana cewa akwai yiwuwar su koma tsaraba da alewa domin burodin ba zai sayu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Rahotanni daga wasu jihohi a Arewacin kasar nan na cewa yanzu haka an fara samun karancin burodi, wanda ke daya daga abubuwan tsaraba.

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

Baya ga tsadar, bincike ya nuna cewa ana samun karancin burodin a wasu sassan jihohin Kano, Katsina da Kaduna.

Burodi
An fara karancin burodi a jihohin Arewa Hoto: Hispanolistic
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa burodi ya kusa kai man fetur karanci, ga kuma tsada domin yanzu haka ya yi tashin gwauron zabo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin burodi ya karu sosai

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa yanzu haka an samu karin farashin burodi da kusan 20%-40% a jihohin Katsina da Kano da Kaduna.

Daya daga cikin masu gidajen burodi a Kaduna ya ce ba wai su na yajin aiki ba ne, amma wasu dalilai sun sanya su dakatar da buga burodin.

Ya danganta karancin buga burodin da tsadar fulawa, inda ya ce buhun da su ke saya N53,000 zuwa N55,000, yanzu ya koma tsakanin N67,000 zuwa N70,000.

"Za mu daina tsarabar burodi," Matafiya

Wasu daga matafiya da ke tsaraba da burodi a Kano sun bayyana damuwa kan yadda farashin burodin ke kara hauhawa.

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Binta Adamu Ibrahim ta shaidawa Legit cewa yanzu haka akwai yiwuwar ta koma yin tsaraba da alewa maimakon burodin.

Saddam Musa Khalid ya shaidawa Legit cewa idan zai je kauyensu na Rimi Sumaila, ya kan yi tsaraba da burodi, amma za a iya samun matsala a yanzu.

An gano gidan burodin 'yan ta'adda

A baya mun ruwaito cewa jami'an tsaron kasar nan sun gano wani gidan burodi da ake bugawa 'yan ta'addan ISWAP burodi a Borno.

Jami'an sojoji karkashin karkashin Operation Hadin Kai ne su ka gano inda ake buga burodin, tare da lalata shi domin rage karfin 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.