Lauyoyi Sun Gano Dalilan Matsalar Najeriya, an Fado Yadda Rashin Tsaro Ya Shafi Mata

Lauyoyi Sun Gano Dalilan Matsalar Najeriya, an Fado Yadda Rashin Tsaro Ya Shafi Mata

  • Kungiyar lauyoyi mata musulmi ta FOMWAN ta bayyana damuwa kan halin da kasa ke ciki, musamman rashin tsaro
  • Wannan na kunshe a sakon shugaba da kakakin FOMWAN, Hajiya Ra’afiah Sanni da Hajiya Maimuna Momodu su ka fitar
  • FOMWAN ta gano cewa mata sun fi kowa shan wahalar tsadar rayuwa, rashin tsaro da hauhawar farashi saboda wasu dalilai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Ondo - Kungiyar lauyoyi mata musulmi ta FOMWAN ta koka kan halin matsin rayuwa da kasar nan ke kara faɗawa a kullum.

Wannan na ƙunshe a cikin sanarwar bayan taron da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabar FOMWAN, Hajiya Ra’afiah Sanni da kakakin kungiyar Hajiya Maimuna Momodu.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya ga illar cire tallafin mai, ya tura sako ga Tinubu akan fetur

Tinubu
Kungiyar FOMWAN ta ce take dokokin Allah ne ya jawo matsalar Najeriya Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa FOMWAN ta ce mata sun fi kowa shiga matsala saboda lalacewar tattalin arziki da tsaro, saboda nauyin da ke komawa kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta shawarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakan shawo kan matsalar tsaro da hauhawar farashin kayan masarufi da ake fama da su.

FOMWAN ta gano dalilin matsalar Najeriya

Kungiyar mata musulmi ta bayyana cewa Najeriya ta fada halin rashin tsaro da wahalar rayuwa ne saboda an juyawa dokokin Allah SWT baya.

Kungiyar ta fadi haka ne a taronta na shekara-shekara karo na 39 da ya gudana a Akure da ke jihar Ondo, inda su ka nuna damuwa kan karuwar matsalolin kasa.

Shugabar kungiyar, Hajiya Ra’afiah Sanni ta ce ya kamata yan kasar nan su koma ga Allah, sannan a dauƙi matakin ilmantar da mata a harkokin siyasar mata.

Kara karanta wannan

Miyagu sun matsa da sace sarakuna, an ɗauke hakimi da ɗiyarsa a Kaduna

An nemi Tinubu ya duba matsalar Najeriya

A baya mun ruwaito cewa jigo a jam'iyyar APC, Hon. Olatunbosun Oyintoloye ya taya ƴan Najeriya mika kukan matsalar tsadar fetur ga shugaban kasa, Bola Tinubu.

Hon. Oyintoloye ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya gaggauta daukar matakan da za su kawo karshen matsalar fetur da ya ƙi ci ya ƙi cinyarsa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.