Zanga Zanga: Izala Ta Saurari Kukan Talakawa, Ta Aikawa Limaman Masallatai Umurni

Zanga Zanga: Izala Ta Saurari Kukan Talakawa, Ta Aikawa Limaman Masallatai Umurni

  • Yan Najeriya sun koka kan yadda malamai suke kira ga matasa kan illar fita zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da ake shirin yi
  • Wasu daga cikin al'umma sun bukaci malamai su dauki wani mataki na musamman maimakon ba al'umma hakuri kawai
  • Legit ta tattauna da wani limamin Izala a karamar hukumar Akko domin jin ko sun fara alkunut kamar yadda aka umurcesu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ba limaman kungiyar umurni kan halin da ake ciki.

Hakan na zuwa ne bayan al'ummar Najeriya sun shiga matsin rayuwa da suke shirin fara zanga zanga a ranar 1 ga Agusta.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

Bala Lau
Sheikh Bala Lau ya yi umurni a fara alkunut. Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa Sheikh Bala Lau ya bayar da umurnin ne a hedikwatar kungiyar Izala da ke Utako a birnin tarayya Abuja kamar yadda Jibwis ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umurnin da Izala ta ba limamai

Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya umurci dukkan limanan kungiyar kan fara alkunut.

Rahotanni na nuni da cewa umurnin ya shafi dukkan limaman Juma'ah na kungiyar da na salloli biyar.

Talakawan Najeriya dama dai sun kasance suna kira ga malamai kan daukan matakin fara alkunut saboda matsin rayuwa da ake ciki.

Izala: Dalilin fara alkunut a jihohi

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa akwai buƙatar komawa ga Allah domin neman mafita ga matsalolin Najeriya.

Saboda haka ya ce za a fara alkunut domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro da sauransu da suka addabi Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ku yi hakuri, ku karawa Bola Tinubu lokaci," Kakakin majalisa ya roki masu shirin zanga zanga

Kungiyar Izala ta umurci shugabannin jihohi

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya umurci dukkan shugabannin kungiyar a jihohi su tabbatar sun fara alkunut da gaggawa.

Haka zalika ya umurce su da yin adduo'i a masallatai, makarantu da sauran wuraren ibada domin samun sauki.

Legit ta tattauna da limamin Izala Gombe

Legit ta tattauna da mataimakin limamin Izala a Sarankiyo da ke Akko a Gombe kan managar alkunut.

Muhammad Babayo ya ce har yanzu ba su fara alkunut ba amma sun samu umurnin shugaban kuma suna shirin farawa.

Kano: An yi alkunut saboda sarauta

A wani rahoton, kun ji cewa magoya bayan sarakuna biyar da gwamnatin jihar Kano ta rattaba hannu aka tube rawunansu sun gudanar da addu'ar alkunut.

An ruwaito cewa an gudanar da sallar tare da yin addu'o'i a kusan dukkanin masarautun da abin ya shafa da fatan maido da sarakunan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng