Matsin Rayuwa Ya Tsananta, Izala Ta Umarci Masallatai a Fara Al Kunut

Matsin Rayuwa Ya Tsananta, Izala Ta Umarci Masallatai a Fara Al Kunut

  • Kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta sanar da fara al-kunut kan halin kuncin da Najeriya ke ciki
  • Shugaban kungiyar na jihar Gombe, Alhaji Salisu Muhammad Gombe ne ya bayar da sanarwar yayin wani taro da suka gudanar
  • Shugaban har ila yau ya yi bayanai na musamman kan malaman da suka gudanar da tafsiri a watan azumin da ya wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Biyo bayan halin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya, kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta sanar da fara al-kunut domin neman sauki.

Jibwis NG
Izala ta sanar da fara al-kunut saboda tsananin rayuwa. Hoto: Freedom Radio Nigeria/Juanmonino
Asali: UGC

Daga ina umurnin Izala ya fito?

Shugaban kungiyar na jihar Gombe, Alhaji Salisu Muhammad Gombe ne ya bada umurnin yayin wani taro da kungiyar ta shirya.

Kara karanta wannan

Jami’an Birtaniya sun yi watsi da Yarima Harry a ziyarar da ya kawo zuwa Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa umurnin ya shafi masallatan kungiyar ne da ake sallolin yau da kullum guda biyar a fadin Gombe.

Shugaba Salisu ya bayar da umarnin ne a yayin taron tattara rahoton yadda tafsirin Ramadan ya gudana a jihar Gombe.

Izala ta fadi dalilin fara Al-kunuti

Cikin dalilan da shugaban ya bayar sun hada da tsadar kayayyaki da suka jefa al'umma da dama cikin kuncin rayuwa.

Ya kara da cewa suna fata yin al-kunut zai sa Madaukakin Sarki Allah SWT ya kawo dauki kan halin da Najeriya ke ciki.

Jawabi kan tafsirin Ramadan

Haka zalika a lokacin taron kungiyar ta tattauna kan yadda take gudanar da ayyukan ta a dukkan yankunan jihar.

Shugaban ya kuma mika godiya ga malaman da suka gabatar da tafsiri a wurare sama da 60 a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Izala ta yi martani kan kashe malami

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake jimamin kisan gillar da aka yi wa Sheikh Hassan Mada a Zamfara, kungiyar Izala ta yi martani kan lamarin.

Kungiyar ta zargi jami'an CPG da hannu a kisan da aka yi wa shugaban majalisar malaman birnin Gusau da ke Zamfara bayan kama wasu 'yan banga 10 da zargin su na da hannun a kisan da aka yi wa shehin malamin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel