Babbar Mota Ta Bi Ta kan Mutane a Wurin Taron Addini, Mutane Sun Mutu a Gombe

Babbar Mota Ta Bi Ta kan Mutane a Wurin Taron Addini, Mutane Sun Mutu a Gombe

  • Babbar motar dakon kaya ta markaɗe mutane har lahira a wurin taron bikin ista a karamar hukumar Billiri a jihar Gombe
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum biyar a hatsarin, wasu da dama sun samu raunuka an garzaya da su asibiti
  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi alhinin waɗanda suka rasu, ya umarci a gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Wata babbar mota ta bi ta kan kiristoci da suka fito bikin ista a garin Billiri da ke ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar mutane biyar da kuma raunata wasu a hatsarin wanda ya faru da safiyar yau Litinin.

Jihar Gombe.
Mota ta markade mutane a wurin taron Ista a Jihar Gombe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce wadanda suka mutu sun hada da maza biyu da mata uku, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mota ta markaɗe mutane a bikin ista

Ya ce bayan waɗanda suka mutu, motar ta raunata wasu mutane takwas da ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe da kuma Asibitin Billiri.

DSP Buhari:

"Wata babbar mota dauke da buhunan hatsi daga jihar Adamawa zuwa Gombe ta samu matsalar birki a lokacin da ta karaso wajen da mabiya addinin Kirista ke taron bikin ista.
"Nan takr motar ta sauka daga kan titi ta bi ta kan masu taron kiristocin ciki har da musulmi waɗanda suka je kallo.

Yadda ƴan sanda su ka kai ɗaukin gaggawa

Buhari Abdullahi ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda daga ofishin Billiri sun kai dauki cikin gaggawa, suka ceto wadanda suka jikkata tare da garzaya wa da su zuwa asibiti domin samun kulawa.

Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun kone motar da ta markaɗe mutanen, suka fasa shaguna sannan suka nufi ofishin ‘yan sanda na Billiri, suna jifar jami’ai da duwatsu da sauran abubuwa masu hadari.

Kakakin ƴan sandan ya kara da cewa:

“DPO da wasu ƴan sanda sun samu raunuka a yayin rikicin. Amma yanzu zaman lafiya ya dawo kamar da, komai ya lafa.
"Rundunar ƴan sanda ta yi Allah-wadai da wannan danyen aiki, tana kuma kira ga jama’a da su zauna lafiya su bar doka ta yi aikinta.”
Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya jajanta faruwar lamarin Hoto: Muhammed Inuwa Yahaya
Asali: UGC

Gwamnan Gombe ya yi alhinin hatsarin

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna alhini da damuwa bisa wannan mummunan hadari.

Ya bayar da umarnin gaggauta binciken musabbabin lamarin tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci, rahoton Leadership.

“Za mu tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan mummunan al’amari," in ji gwamna.

Mawaƙan yabo 4 sun mutu a Ogun

A wani labarin, kun ji cewa fitattun mawakan addinin kirista huɗu sun rasa rayuwansu a wani hatsari da ya rutsa da su a Ogun.

Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Ogun, Florence Okupe, ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Wadanda aka rasu sun hada da, Evangelist Ayodeji Kekerejesu, Evangelist Iyanu Joseph, Monjolajesu Oluwapamilerin da Opeyemi Adesina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262