Tura Ta Kai Bango: Mazauna Kaduna sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, An Rage Mugun Iri a Gari

Tura Ta Kai Bango: Mazauna Kaduna sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, An Rage Mugun Iri a Gari

  • Mazauna jihar Kaduna sun ba 'yan ta'adda kashi yayin da su ka kai masu hari kauyen Rugar Sojidi a karamar hukumar Kagarko
  • Da farko dai 'yan bindigar sun sace mutane uku, lamarin da ya fusata mazauna kauyen har suka yi karfin hali tare da yin zazzafan martani
  • Rundunar 'yan sanda mazauna kauyen sun yi namijin kokari tare da afkawa 'yan ta'addan har suka yi nasarar kashe guda daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna- Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun fara daukar matakin kare kansu yayin da suka fatattaki 'yan ta'adda.

Rahotanni sun ce 'yan ta'adda sun kai hari kauyen Rugar Sojidi da Fulani ke zaune a kusa da Issan Makaranta da ke karamar hukumar Kagarko a Kaduna.

Kara karanta wannan

Harin bam: Rundunar sojojin Najeriya ta fadi yadda za ta yi da 'yan ta'adda

Kaduna
Mazauna Kaduna sun kashe daya daga cikin 'yan ta'adda da ya kai masu hari Hoto: Legit
Asali: Original

Daily Trust ta tattaro cewa sai da 'yan bindigar su ka sace mutane uku daga kauyen kafin mazauna yankin su dauki mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan garin Kaduna sun rage mugun iri

Fulani mazauna Rugar Sojidi a karamar hukumar Kagarko, Kaduna sun kashe dan ta'adda daya.

Hakan ya faru ne bayan miyagun sun kai masu hari tare da sace akalla mutane uku daga kauyen kamar yadda suka saba a wasu kauyukan.

'Yan sanda sun tabbatar da harin 'yan bindiga

A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya fitar, ta tabbatar da harin.

Ya ce rundunar 'yan sanda ta kai dauki ga mazauna garin amma ta tarar sun fatattaki yan ta'addan har sun kashe daya daga cikinsu.

Kakakin ya kara da cewa an ceto dukkanin mutane ukun da aka sace, sannan an samu alburusai da bindiga kirar AK-47 da miyagun su ka gudu su ka bari.

Kara karanta wannan

Bayan tashin bama-bamai a Borno, sojoji sun kashe 'yan ta'adda har maboyarsu

An kama mata da zargin taimakon 'yan bindiga

A wani labarin kun ji cewa rundunar sojojin Nigeriya ta cafke wasu mata guda uku da ake zargi da yiwa 'yan ta'adda leken asiri a Kaduna.

An kama matan da ke fakewa da tallan zuma a bakin titin ne a kauyen Dogon Daji a karamar hukumar Kagarko a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel