Asiri Ya Tonu: An Gano Ministan Bogi Mai Ƙoƙarin Damfara Ta WhatsApp

Asiri Ya Tonu: An Gano Ministan Bogi Mai Ƙoƙarin Damfara Ta WhatsApp

  • Ministan ma'adanai na kasa, Dele Alake ya tona asirin wani babban dan damfara mai kokarin cutar mutane da sunansa
  • An gano cewa dan damfarar yana amfani da wata lambar wayar hannu ta kafar WhatsApp wajen cutar al'umma da sunan shi minista ne
  • Alake ya bayyana irin dabarun da mutumin yake yi da kuma lambar wayar da yake amfani da ita wajen turawa mutane saƙonni

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan ma'adanai na kasa Dele Alake ya ankarar da al'umma kan wani dan damfara mai amfani da sunansa.

Dele Alake ya bayyana cewa dan damfarar na amfani da kafar WhatsApp ne domin cutar mutane.

Kara karanta wannan

Kotu ta tasa keyar 'Sanata' zuwa kurkuku saboda zargin damfarar 'yar kasar waje

Dele Alake
Minista ya gargadi mutane kam mai damfara da sunansa. Hoto: Dele Alake
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mai taimakawa ministan na musamman, Segun Tamori ne ya bayyana lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan damfarar ke kokarin cutar mutane

Cikin sakon da Segun Tamori ya wallafa a jiya Laraba ya nuna cewa dan damfarar yana amfani da lambar wayar 07077437582.

Ya kara da cewa dan damfarar yana ikirarin cewa shi ne ministan ma'adanai, Dele Alake domin ya cuci al'umma.

Ministan ma'adanai ya gargadi jama'a

Cikin gaggawa ministan ma'adanai ya gargadi mutane cewa ba shi da alaka ta kusa ko ta nesa da mutumin, rahoton Channels Television.

Dakta Dele Alake ya kuma yi kira ga mutane kada su yarda da duk wani sako da za a tura musu ta WhatsApp da sunan shi ne.

Matakin da ministan ya dauka

Har ila yau, ministan ya ce ya ba jami'an tsaro umurnin binciko wanda yake aikin domin ganin an hukunta shi.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Alake ya kuma shawarci al'umma su saka ido domin ganin ba su fada tarkon yan damfara irin mutumin nan ba.

Sojoji sun yi kira ga 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi kira na musamman ga kungiyoyin 'yan ta'adda da tsagerun da suka dauki makami domin yaki da gwamanti.

Babban hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya yi kiran a jiya Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng