'A Rabu da Fetur,' Jagora a APC Ya ba Tinubu Lakanin da Najeriya Za Ta Samu Kudi

'A Rabu da Fetur,' Jagora a APC Ya ba Tinubu Lakanin da Najeriya Za Ta Samu Kudi

  • Jagora a jam'iyyar APC ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dabarun habaka tattalin arzikin Najeriya ba tare da man fetur ba
  • Olatunbosun Oyintoloye wanda jigo ne a jam'iyyar reshen jihar Osun ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan albarkatun teku
  • Ya bayyanawa manema labarai a Osogbo cewa an gano za a iya samun dala biliyan 20 duk shekara daga bangaren tare da samar da aiki miliyan 2

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun-Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintoloye ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan dabarun samun karin arziki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda, an kamo miyagu a Abuja da Oyo

Ya bayyana dabarun a Osogbo yayin tattaunawa da manema labarai, inda ya ce ya kamata a rage dogaro da man fetur.

Bola Ahmed Tinubu
Jagora a APC ya bawa Shugaba Tinubu dabarar habaka arzikin Najeriya Hoto: Ajuri Ngalele
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa jigon jam'iyyar ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan albarkatun da ake samu a teku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Za a samu $20b duk shekara,' Oyintoloye

Jagora a jam'iyya mai mulki na APC ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa samar da ma'aikatar kula da albarkatun teku da arzikin da ake samu a bangaren.

Ya ce ministan ma'aikatar, Gboyega Oyetola ya gano cewa bangaren zai rika samar da $20b duk shekara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya wallafa cewa Oyintoloye na ganin za a iya kara habaka bangaren domin rage dogaro da man fetur.

Ya kara da cewa amma dole sai an samar da tsarin kudi da samar da kudaden gudanar da wasu ayyukan kamar bunkasa yawon bude ido a bangaren tekunan kasar nan.

Kara karanta wannan

'Za mu hadu a kotu,' Jigon APC ya yi barazana kan nadin Abdullahi Ganduje

Rance daga CBN: Gwamnati ta fara bincike

A baya mun ruwaito muku cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta jagoranci binciken rancen da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ciwo daga CBN.

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ci bashin Naira tiriliyan 23 domin gudanar da wasu ayyuka, lamarin da gwamnati ta ce za ta biya amma za ta bincika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.