'Mutuwar' Wani Matashi Kabiru Sakamakon Azabtarwar Yan Sanda Ya Tada Ƙura a Najeriya

'Mutuwar' Wani Matashi Kabiru Sakamakon Azabtarwar Yan Sanda Ya Tada Ƙura a Najeriya

  • Ana zargin jami'an ƴan sanda sun yi sanadin mutuwar wani matashi, Kabiru Ibrahim a kauyen Soro a jihar Bauchi
  • Kungiyar kare haƙkin ɗan adam, Amnesty, ta bayyana cewa ƴan sanda sun aikata wannan mummunan laifin ne kan wanda ake zargi da sata
  • Wannan lamari dai ya harzuka ƴan Najeriya inda suka yi ruwan martani a kafafen sada zumunta kan mutuwar Kabiru Ibrahim

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Fitacciyar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam Amnesty International ta buƙaci hukumomi su gudanar da bincike kan kisan Kabiru Ibrahim a Soro, jihar Bauchi.

Ana zargin Kabiru ya mutu ne sakamakon mugun duka na rashin imani da azabtarwar da ƴan sanda suka masa bisa zargin satar ledar taliyar indomi.

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Kabiru Ibrahim da yan sanda.
Amnesty ta ce yan sanda ne suka yi ajalin Kabiru Ibarahim sakamakon azabtar da shi Hoto: @AmnestyNigeria, Nurphoto
Asali: UGC

Kabiru ya mutu a asibitin Bauchi

Matashin ya rasu ne ranar 11 ga watan Mayu, 2024 a asibitin koyarwa na jihar Bauchi sakamakon take haƙƙin ɗan adam da ƴan sanda suka yi a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X cewa:

"Binciken da muka yi ya nuna mana cewa ƴan sanda sun azabtar da shi sosai saboda danginsa sun gaza biyan kudin da za a sasanta al'amarin."

Ƴan Najeriya sun fusata da mutuwar Kabiru

Bayan kalaman ƙungiyar Amnesty International, ƴan Najeriya sun fusata da abin da aka yi wa Kabiru Ibrahim a manhajar X.

Kwamared Deji Adeyanji ya ce:

"Wannan babban abin takaici ne."

@ostelly ya ce:

"Rai ba a bakin komai yake ba ga kuma rashin kwarewar waɗanda ake kira jami'an tsaro."

@Pillarkomputers ya mayar da martani da cewa:

Wannan abin tausayi ne kuma mugunta ce tsantsa, ba ruwan Allah a wannan lamarin."

Kara karanta wannan

Bayan kashe sojoji, ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 80 a Katsina

@JJerry55336 ya ce:

"Satar kananan abubuwa laifi ne yayin da satar dukiyar jama'a ke jawo kyaututtuka da kariya daga hukumomin tsaro. Ya kamata mu sauya ma'anar laifi a Najeriya."

Sojoji sun daƙile hari a Kaduna

A wani rahoton kuma Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun halaka ɗan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Gwarazan sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar ne yayin da suke hanyar zuwa kai hari kan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel