Al Mustapha Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Lalata Tsaro a Najeriya, Ya Kawo Mafita
- Tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi magana a kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya
- Al-Mustapha ya ce babban matsalar da aka samu kan rashin tsaro a Najeriya laifin Shugabannin baya ne da suka gaza yin wani abu
- Tsohon sojan ya koka kan yadda aka bar matsalar ta girma har zuwa yadda ba za a iya dakile ta da sauki ba, inda ya ce sai dai ayi amfani da kimiyya da dabaru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Manjo Hamza Al-Mustapha ya magantu kan yadda matsalar tsaro ya tabarbare a Najeriya.
Hamza Al-Mustapha ya ce matsalolin tsaro da ke fuskantar Najeriya laifin shugabannin da suka gabata ne.
Hamza Al-Mustapha ya zargi shugabanni da sakaci
Tsohon dogarin Marigayi Sani Abacha ya ce wadanda ke da alhakin tsare jama'a da kawo zaman lafiya sun gaza yin katabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana haka yayin wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Abuja, cewar rahoton The Guardian.
Ya ce wannan matsala da ake ciki na rashin tsaro yana bukatar amfani da dabarun kimiyya domin dakile matsalar.
"Musabbabin rashin tsaro"- Al-Mustapha
Har ila yau, ya ce babban matsalar ita ce shugabannin da suka gabata sun gaza aiwatar da wani abu kan nauyin da aka daura musu yadda ya kamata.
Al-Mustapha ya ce rashin tsaron Najeriya da sauran ƙasashen Afrika an yi watsi da su tun da dadewa.
Tsohon sojan ya ce barin matsalar ya jawo kara dagula lamura a kasar wanda ya wuce gona da iri.
Al-Mustapha ya magantu kan tsadar fetur
A wani labarin, kun ji cewa Hamza Al-Mustapha ya yi wata magana da ta za ta iya zama hannunka mai sanda ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya nuna sai an yi hattara da ‘yan kasuwa.
Al-Mustapha mai ritaya a wata hira da ya yi da ƴan jaridu ya ce masu harkar fetur za su iya rusa gwamnati gaba ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng