Hamza Al-Mustapha Na Iya Samun Mukamin Kwamandan NSCDC a Gwamnatin Tinubu

Hamza Al-Mustapha Na Iya Samun Mukamin Kwamandan NSCDC a Gwamnatin Tinubu

  • Shugaba Tinubu na ci gaba da nade-naden mukamai musamman a bangaren tsaro wanda shi ne kingishin zaman lafiya a kasar
  • Ana hasashen a wannan karo Mejo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ka iya samun mukami a bangaren tsaron kasar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai alamun Tinubu ya nada shi kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC a kasar

FCT, Abuja - Akwai alamun Shugaba Tinubu ya nada Mejo Hamza Al-Mustapha mai ritaya a matsayin Kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC.

The Guardian ta tattaro cewa Al-Mustapha na daga cikin wadanda Tinubu zai yi aiki da su don gyara matsalar tsaro a kasar.

Akwai hasashen Tinubu ya nada Al-Mustapha kwamandan NSCDC
Akwai hasashen Hamza Al-Mustapha ya samu mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: Hamza Al-Mustapha, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Wane shiri Tinubu ke da shi kan Al-Mustapha?

Rahoton ya ce Tinubu na iya tafiya da Al-Mustapha ganin irin kwarewarshi a bangaren da ya shafi tsaro da ta zama babbar barazana ga kasar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan kuma na iya faruwa ganin yadda Tinubu ke nada mukamai a gwamnatinsa ba tare da nuna bambancin jam'iyya ko siyasa ba.

Idan ba a mantaba, jigon jam'iyyar PDP, Nyesom Wike a yanzu shi ne ministan birnin Tarayya, Abuja a gwamnatin Tinubu ta APC.

Waye Al-Mustapha a Najeriya?

Al-Mustapha shi ne shugaban masu tsaron tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha da ya rasu a 1998.

Har ila yau, ya tsaya neman shugabancin kasar a jam'iyyar AA inda ya koka kan yadda tsohon shugaban kasa, Buhari ya rikirkita lamarin tsaro.

Yayin da ya ke ya ke garabar da jawabi kafin gudanar da zaben 2023, Al-Mustapha ya ce Najeriya ta na zaune ne a kan bam wanda zai iya fashewa a kowa ne lokaci.

Ya koka kan yadda makamai ke yawo a kasar da kuma safarar miyagun kwayoyi musamman tsakanin matasa.

Kara karanta wannan

Imam Ibrahim Kashim: Dan Jigon PDP Dan Shekara 24 Da Tinubu Ya Nada Shugaban FERMA

Tinubu ya nada shugaban EFCC, Ola Olukoyede

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar EFCC bayan dakatar da tsohon shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa.

Tinubu ya nada Ola Olukoyede wanda kwararren lauya ne kuma zai shafe wa'adin shekaru hudu bayan majalisa ta tantance shi.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya dakatar da Bawa kan zargin badakala a hukumar da ya jagoranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel