BOUESTI: Jami'a Ta Kori Ɗalibai Mata 2 Kan Bidiyon da Ya Fito, Yan Sanda Sun Fara Bincike

BOUESTI: Jami'a Ta Kori Ɗalibai Mata 2 Kan Bidiyon da Ya Fito, Yan Sanda Sun Fara Bincike

  • Jami'ar BOUESTI ta kori ɗalibar da aka gani a faifan bidiyo tana dukan abokiyar karatunta da wadɗa ta samo bulala
  • Wannan mataki na zuwa ne yayin da rundunar ƴan sandan jihar ta fara gudanar da bincike kan lamarin da nufin gurfanar da mai laifin a kotu
  • Faifan bidiyon wanda ya watsu a kafafen sada zumunta ya harzuƙa mutane da dama, lamarin da ya ja hankalin mahukunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti -Hukumar Jami’ar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Bamidele Olumilua Ikere-Ekiti (BOUESTI) ta kori dalibar da aka gani a bidiyo tana bugun ƴar uwarta ɗaliba.

A wani faifan bidiyo da ya bazu ranar Litinin a manhajar X watau Twitter, an ga ɗalibar da bulala a hannu ta lakaɗawa abokiyar karatunta dukan tsiya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki wasu matakai na ƙawo ƙarshen satar ɗalibai da tsaro a Najeriya

Jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Ekiti.
An kori ɗalibar da aka gani a bidiyo tana bugun ƴar uwarta daliba a jihar Ekiti Hoto: Bamidele Olumilua University of Education, Science and Technology Ikere-Ekiti
Asali: Facebook

Dalibar jami'a ta lakadawa wata duka

A bidiyon, an ji ɗalibar da ta aikata laifin ta ɗaga murya tana faɗa wa wanda take bugu da bulala cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina son na ga yadda z aki rama, ba kin kira ni da ƴar iska ba, saboda kin ga na yi shiru ko? Sai na zubar miki da jini yau kuma ba wanda ya isa ya hana ni."

Haka nan an ga ɗalibar da ake bugun tana gudun neman tsira yayin da mai laifin kuma ta ci gaba da binta tana zabga mata bulala.

Bidiyon ya kuma ɗauki mutane da yawa da ke wurin amma babu wanda ya yi ƙoƙarin raba faɗan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Wannan bidiyo dai ya harzuƙa mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda mafi akasari suka yi kira ga jami'ar ta gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi martani kan zargin neman cin hancin $150m a hannun Binance

Jami'ar Ekiti ta kori ɗalibai 2

A farko mai magana da yawun jami'ar, Tope Akinbisoye, ya ce kwamitin ladabtarwa na makaranta ya kira ɗalibar da ta aikata laifin domin fara bincike.

Amma a wata sanarwa ranar Talata, jami'ar ta sanar da korar ɗalibar da ta aikata laifin mai suna, Opemiposi Precious Bolaji, yar shekara 18 da ke karatun aikin jarida.

An kori ɗalibar ne tare da Genesis Osaro, wadda ta samo sandar da aka yi amfani da ita wajen lakaɗawa Gloria Ajayi, dukan kawo wuƙa a bidiyon.

"Jami'ar mu ba zata lamurci duk wani nau'i na rashin da'a ba kuma mun yi alkawarin samar da yanayi mai aminci da hadin kai ga dukkan mambobin Jami'ar," in ji sanarwar.

Ƴan sanda sun fara bincike a jami'ar

Adeniran Akinwale, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ekiti, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishinan ya umurci kwamandan yankin Ikere ya haɗa kai da jami'ar wajen gano ɗalibar da ta aikata laifin sannan a binciketa kana a gurfanar da ita a kotu.

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Masu garkuwa 8 sun shiga hannu

A wani rahoton kuma jami'an 'yan sanda a jihar Ekiti sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane takwas tare da sheke daya daga cikinsu.

'Yan bindigar da aka kama sune suka yi garkuwa da wasu yaran makaranta da malamansu a yankin Emure-Ekiti a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel