Majalisa Ta Ɗauki Wasu Matakai Na Kawo Ƙarshen Satar Ɗalibai da Tsaro a Najeriya

Majalisa Ta Ɗauki Wasu Matakai Na Kawo Ƙarshen Satar Ɗalibai da Tsaro a Najeriya

  • Majalisar wakilan ta ɗauki wasu matakai da nufin kawo karshen satar ɗalibai a makarantu da dawo da tsaro a Najeriya
  • Ta umurci kwamitocinta da suka shafi hukumomin tsaro da na tsaro su zauna da hafsoshin tsaron ƙasar nan domin lalubo mafita mai ɗorewa
  • A wasu shekaru da suka gabata dai an sha fama da yawan kai hari da garkuwa da ɗalibai a makarantu musamman a jihohin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta nuna damuwa kan yawaitar kai hare-haren garkuwa da mutane da asarar rayuka a makarantun gida Najeriya.

Majalisar ta koka kan yawan samun lamarin satar ɗalibai, asarar rayuƙa da lalata kadarori a makarantu tun shekarar 2014, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki bayan kwashe kwanaki a kauyen da aka kashe jami'ai

Majalisar wakilan tarayya.
Majalisar tarayya ta bukaci a kawo ƙarshen satar ɗalibai a makarantun Najeriya Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan kudirin gaggawa da Honorabul Billy Osawaru ya gabatar a zaman mambobin majalisar ranar Laraba a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da majalisa ta ɗauka

Bayan amincewa da kudirin, majalisar ta wajabtawa kwamitocinta na rundunar sojin ƙasa, sojin ruwa, sojin sama, ƴan sanda da kwamitin tsaro su zauna da hafsoshin tsaro.

Ta ɗora wa waɗannan kwamitoci alhakin tattaunawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan domin lalubo hanyar tabbatar da tsaro a makarantu.

Haka nan kuma majalisa ta buƙaci su nemo hanyar magance ƙalubalen tsaron da ya addabi ƙasar nan domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Majalisa tayi kira ga makarantu

Bugu da ƙari, majalisar wakilai ta shawarci makarantu su yi aiki da jami'an tsaro masu zaman kansu domin taimakawa hukumomin tsaro wajen tsare makarantu.

‘Yan majalisar sun kuma yi kira da a sake wayar da kan jama’a musamman ga yaran da ba su zuwa makaranta waɗanda har yanzu suna rayuwa ne a cikin fargaba.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna ya ɗauki zafi yayin da APC ta umurci majalisa ta tsige shi nan take

A shekarun baya-bayan nan dai an sha fama da yawaitar hare-haren garkuwa da ɗalibai a makarantu da dama a kasar nan.

Galibi an fi samun irin waɗannan hare-hare a jihohin Borno, Nasarawa, Neja, Zamfara, Katsina da Kaduna, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Gwamna Fubara ya hana ciyamomi zuwa majalisa

A wani rahoton na daban Gwamna Simi Fubara ya hana ciyamomi da dukkan jagororin kananan hukumomi 23 bayyana a gaban majalisar dokokin Ribas.

Wannan mataki na zuwa ne awanni 24 bayan APC ta umurci majalisar ta fara shirin tsige Fubara daga kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel