A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango

A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango

  • Ana tsaka da soyewa a daren farkon wasu ma'aurata, ciwon zuciya ya kashe amarya har lahira
  • Masoyan biyu 'yan asalin kasar Brazil sun yi aure amma a daren farko amarya ta fara alamun rashin lafiya
  • Bayan ango ya kira masu taimakon gaggawa, ana kan hanyar asibiti amarya mai shekaru 18 ta rasu

Ibirite, Brazil

Angwancin wata amarya mai shekaru 18 da angonta mai shekaru 29 ya tsinke bayan amarya ta samu ciwon zuciya kuma ta mutu yayin da suke saduwa a daren farko.

Kamar yadda The Sun ta ruwaito, amaryar ta fara nuna alamun rashin lafiya kuma ta fadi a gidansu dake garin Ibirite a Brazil a yammacin Alhamis.

Lamarin ya faru ne bayan ma'auratan sun yi aure kuma suna wani shagali a gonar mijin, Pulse ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Kwanturolan Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano

KU KARANTA: Dan sanda a Yobe ya fashe da kuka, ya bayyana azabar da suke sha wurin Boko Haram

A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango
A daren farko, amarya mai shekaru 18 ta sheka lahira suna tsaka da soyewa da ango. Hoto daga pulse.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

KU KARANTA: Katuwar Giwa ta Fada Gidan Wata Mata Neman Abinci, Jama'a Sun Dinga Mamaki

An gano cewa amaryar ta fara alamun rashin lafiya kuma mijin ya kira makwabtansa domin taimako sannan ya tari direban tasi ya kaita asibiti amma ya ki.

Ango ya nemi masu taimakon gaggawa

Ya yanke shawarar kiran taimakon gaggawa daga asibiti. Bayan dogon jira an kawo masa taimako daga asibiti kuma sun samu matar tana kokawa da numfashinta, lamarin da yasa suka ce zuciya ce matsalarta.

Amarya ta rasu kan hanyar zuwa asibiti

Cike da takaici tare da alhini, ana kan hanyar kai sabuwar amaryar asibiti tace ga garinku

An gano musabbabin mutuwar amarya

Bayan duba gawarta, babu wata alama ta fada ko wani abu makamnacin hakan, amma wata makwabciyarsu tace bata ji ihu ko wani sauti ba na nuna alamar ma'auratan fada suka yi.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Bayan sake duba gawar, an gano cewa amaryar tana da matsala a hanyar numfashinta kuma mutuwa tayi ba kasheta aka yi ba.

Angon cike da alhini da dimuwa ya fada bakin ciki sakamakon mutuwar amaryarsa wacce ta kasance masoyiyarsa. Ya ce baya tsammanin zai cigaba da rayuwa a kasar Brazil.

A wani labari na daban, an baiwa wata dalibar Najeriya takardar dakatarwa daga kwaleji saboda bata fito tarar shugaban kasan Najeriya ba a ziyarar da ya kai jihar Borno a ranar 17 ga watan Yuni.

Wani shafi mai amfani da Instabog9ja ya wallafa takardar dakatarwan wacce ta fara aiki daga ranar 21 ga watan Yuni.

Dakatarwan za ta kai har na mako daya. A wata takardar da kwalejin koyar da jinya da ungwan zoma ta Maiduguri ta fitar, an umarci dalibar da ta dawo mako na gaba da iyayenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel