Tudun Biri: An Fara Muhimman Ayyuka 3 a Kauyen da Sojoji Suka Yi Kuskuren Jefa Bam a Taron Maulidi

Tudun Biri: An Fara Muhimman Ayyuka 3 a Kauyen da Sojoji Suka Yi Kuskuren Jefa Bam a Taron Maulidi

  • Watanni bayan kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi, Malam Uba Sani ya fara cika alƙawurran da ya ɗaukar wa kauyen Tudun Biri
  • A watan Disamba ne sojoji suka jefa bam kan masulmi a taron Maulidi a kauyen, lamarin da ya yi ajalin mutane sama da 150
  • Gwamna Sani ya ce gina titi, asibiti da wurin koyon sana'a na ɗaya daga cikin ayyukan da zasu inganta rayuwar mutanen kauyen

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya kaddamar da fara muhimman ayyuka uku a kauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.

Daga cikin ayyukan da gwamnan ya kaddamar da farawa har da ginin titi mai tsawon kilomita 5.5 wanda ya haɗa ƙauyen da titin zuwa filin jirgin sama na jihar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Gwamnatin Kaduna ta fara cika alƙawarin ta ɗauka a kauyen Tudun Biri Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Gwamnan ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin ayyukan da aka fara a Tudun Biri

Ya jero ayyukan da aka fara a kauyen, ga su kamar haka:

- Gina titi mai tsawon kilomita 5.525 daga unguwar Tudun Biri zuwa titin filin jirgin sama.

- Gina asibitin kula da lafiya a matakin farko (PHC) na farko a Tudun Biri, da;

- Gina cibiyar koyon sana'o'i da fasahar zamani.

Waɗannan ayyuka na zuwa ne biyo bayan ibtila'in da ya afku ranar 3 ga watan Disamba, 2023 lokacin da sojoji suka yi kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi a Tudun Biri.

Bayan haka ne gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da ‘yan Najeriyan da suka nuna damuwa suka ba da gudummawar kuɗade masu yawa don sake gina ƙauyen da tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Gumi ya taka rawa wurin kubutar da dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani ya fayyace gaskiya

Tudun Biri: Gwamna ya fara cika alƙawari

Da yake jawabi a wurin kaddamar da fara aikin, Gwamna Sani ya ce aikin titin zai inganta hanyoyin safara ga manoman garin tare da saukaka sayar da kayan amfanin gona.

Malam Uba Sani ya ce:

"Kwana biyu bayan kuskuren jefa bam, na yi alƙawarin cewa idan Allah ya yarda za mu gina ababen more rayuwa ga al'ummar Tudun Biri, mu gina muku titi, asibiti da cibiyar koyon sana'o'i.
"Kuma da izinin Allah yau ga shi mun zo muna ƙoƙarin cika wannan alƙawari."

Alhaji Aminu Idris Hakimin Rigasa ya bayyana godiya a madadin al’ummar Tudun Biri bisa cika alkawarin da gwamnan ya dauka.

Yadda aka magance satar ɗalibai a Borno

A wani rahoton na daban Gwamna Zulum ya bayyana dalilin da ya sa aka jima ba a ji ƴan ta'adda sun sace dalibai daga makarantu a jihar Borno ba.

Farfesa Babagana Zulum ya ce shirin samar da aminci a makarantu da suka kaddamar shekaru 7 zuwa 8 da suka wuce ya yi aiki yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel