Gumi Ya Taka Rawa Wurin Kubutar da Dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani Ya Fayyace Gaskiya

Gumi Ya Taka Rawa Wurin Kubutar da Dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani Ya Fayyace Gaskiya

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa babu hannun Sheikh Ahmed Gumi a sakin daliban makaranta
  • Uba Sani ya ce kuma babu kamshin gaskiya kan cewa an biya kudin fansa kafin sakin yaran makarantar a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan sace daliban 137 a ranar 7 ga watan Maris a makarantar Kuriga da ke jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi magana bayan kubutar daliban makarantar firamare a jihar.

Sani ya ce babu wata rawa da Sheikh Ahmed Gumi ta taka wurin tabbatar da dawowar daliban cikin koshin lafiya.

Uba Sani ya yi martani kan saka hannun Gumi a kubutar da dalibai 137
Uba Sani ya ce babu abin da Gumi ya tsinana wurin ceto dalibai 137 a Kaduna. Hoto: Ahmed Gumi, Uba Sani.
Asali: Facebook

Martanin Uba Sani kan gudunmawar Gumi

Kara karanta wannan

Ana alhinin mutuwar dalibai a Nasarawa, mata 4 sun mutu yayin karbar zakka a Bauchi

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yammacin yau Lahadi 24 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk da malamin ya so ya jagoranci sulhu domin kubutar da yaran amma babu wata gudunmawarsa a ciki.

Ya kara da cewa yaran 137 da aka sace a ranar 7 ga watan Maris an kubutar da su ne ta taimakon jami'an tsaro a jihar Zamfara.

Har ila yau, gwamnan ya karyata jita-jitar da ake cewa an biya kudin fansa domin ceto yaran daga hannun 'yan bindiga.

"Duk abin da kuke ji shaci-fadi ce kawai na mutane, zan fada maka babu wani tsoron kuskure babu hannun Gumi a wannan lamari."

- Uba Sani

Uba Sani ya tura sakon jaje

Gwamnan ya kuma ce kamar yadda ake yadawa, dalibai 137 aka sace ba 287 kamar yadda wasu ke fada.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya karyata masu jita-jita cewa ya ware N6bn don ciyar da Kanawa a Ramadana

Sai dai gwamnan ya bayyana takaicinsa yayin da daya daga cikin malaman da aka sace daliban tare da shi ya rasu.

Uba Sani daga bisani ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin tare da jajantawa iyalan daliban makarantar.

An ceto daliban makaranta a Kaduna

Kun ji cewa Daliban makarantar Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna da aka sace sun shaki iskar ‘yanci.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya tabbatar da haka inda ya ce ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da wadannan yara sun fito da su.

Wannan na zuwa ne bayan sace daliban da aka yi a ranar 7 ga watan Maris a jihar wanda ya ta da jijiyoyin wuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel