Gwamnatin Sojar Burkina Faso Ta Dakatar da Wasu Gidajen Jaridu Daga Kasar

Gwamnatin Sojar Burkina Faso Ta Dakatar da Wasu Gidajen Jaridu Daga Kasar

  • Kasar Burkina Faso ta sanar da dakatar da manyan gidajen rediyon BBC da VOA daga watsa labarai a kasar
  • An ruwaito cewa sanarwar ta fito ne daga ofishin sojojin da ke mulkin kasar a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu
  • A cikin sanarwar sojojin sun bayyana dalilan da suka sa dakatarwar tare da fadin lokacin da za sujanye ta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Burkina Faso sun dakatar da gidajen rediyon BBC da Muryar Amurka daga gudanar da shirye-shirye a kasar.

Burkina Faso
Burkina Faso ta zargi BBC da VOA da yada labarin karya. Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Dakatarwar ta biyo bayan yada rahoton da gidajen rediyon suka yi ne a kan harin da ake zargin sojojin da kaiwa kan fararen hula.

Kara karanta wannan

Nasrun MinalLah: Dakarun sojoji sun daƙile hari, sun sheƙe ƴan bindiga a ƙauyen Taraba

A wani rahoton da jaridar Al-Jazeera ta fitar ya nuna cewa sojojin sun kashe akalla mutane 223 ciki harda yara 56.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatarwar za ta kai yaushe?

A ranar Alhamis ne dai hukumar sadarwar kasar ta sanar da dakatar da manyan gidajen rediyon na sati biyu, cewar jaridar Reuters

Me yasa aka dakatar da BBC da VOA?

A cewar sanarwar da sojojin suka fitar, an dakatar da gidajen rediyon ne saboda cin fiska ga kasar wurin ruwaito cewa sojojin sun ci zarafin fararen hula.

Sojojin sun ce labarin ba shi da inganci kuma gidajen rediyon sun yi gaggawa wurin rashin tuntubar gwmantin domin jin gaskiyar lamarin.

An yi yunkurin juyin mulki a Burkina Faso

A wani rahoton kuma, ku ji cewa sojin da ke mulki a Burkina Faso sun sanar da yunkurin juyin mulki da wasu sojoji su ka yi

Kara karanta wannan

"Babu riba": Kamfanonin sadarwa a Najeriya suna shirin ƙara kudin data, kira da SMS

Sojin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa inda su ka ce an kama sojoji hudu kan zargin cin amanar kasa

An kashe 'yan ta'adda a Burkina Faso

A wani rahoton kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda na musamman, sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 40 a ƙasar Burkina Faso

Lamarin dai ya faru ne a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar bayan tafka artabu tsakanin rundunar 'yan sandan da 'yan ta'addan

Asali: Legit.ng

Online view pixel