Yadda Aka Bi Har Gida Aka Kashe Wata Uwa Tare da Raunata ‘Diyarta a Jihar Arewa

Yadda Aka Bi Har Gida Aka Kashe Wata Uwa Tare da Raunata ‘Diyarta a Jihar Arewa

  • A wani lamari mai kama da gisan gilla, an tsinci gawar wata mata a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa
  • An gano gawar matar dauke da alamun yanka a wuya da kai a cikin falonta bayan an fasa kofar gidan nata
  • Da yake tabbatar da lamarin, kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce an kuma gano 'diyar matar cikin wani hali da raunuka

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Jigawa - Rahotanni sun kawo cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun bi har gida sun sheke wata mata sannan suka raunata 'diyarta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

A cewar kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, marigayiyar mai suna Esther Adekanla tana zaune ne a tsallaken gidan man Awajil, wadda aka fi sani da Hadiza Nakowa Dutse

Kara karanta wannan

Sabuwar takaddama yayin da ake zargin mutuwar dan siyasa a hannun jami'an tsaron CPG a jihar Arewa

An tsinci gawar wata mata a jihar Jigawa
Yadda Aka Bi Har Gida Aka Kashe Wata Uwa Tare da Raunata ‘Diyarta a Jihar Arewa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Gani na karshe da aka yi mata ya kasance a ranar 12 ga watan Fabrairu, wanda hakan ya jefa makwabtanta cikin zargi kuma duk kokari da aka yi na kiran layukan wayanta ya ci tura, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan sanda suka gano gawar wata mata a Jigawa

DSP Adam ya ce jami'an 'yan sandan Dutse sun shiga aiki nan take bayan sun samu rahoton lamarin, sannan suka garzaya gidanta, inda da zuwansu suka lura da shi a rufe.

Ya ce an fasa kofar gidan inda aka tsinci gawar marigayiyar a falon gidan.

Har ila yau, kakakin 'yan sandan ya ce an lura da yanka a kai da wuyan matar yayin da jikinta ya fara rubewa.

'Diyar matar na asibiti cikin wani hali

Adam ya ce an tsinci diyarta mai suna Christiana Michael, 'yar shekaru 11 rufe a dakin ajiye kaya kanta da rauni, a raye amma tana cikin wani yanayi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kona mutane 12 har lahira, sun kuma babbake gidaje 17 a wata jihar Arewa

Mai magana da yawun 'yan sandan ya kara da cewar an gaggauta kai gawar da yarinyar zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni.

A cewarsa, wani likita ya tabbatar da mutuwarta yayin da aka kai gawar zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano don gwaji, rahoton New Telegraph.

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah a Taraba

A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki kauyuka uku a karamar hukumar Zing ta jihar Taraba.

Yayin harin da aka kai a daren Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, maharan sun yi garkuwa da mutane 16 ciki harda wani malamin addini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel