Nade-Naden Mukamai: Majalisar Dattawa Ta Amince da Muhimmiyar Bukatar Tinubu

Nade-Naden Mukamai: Majalisar Dattawa Ta Amince da Muhimmiyar Bukatar Tinubu

  • Majalisar Dattawa a Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu da ya nema a wurinta a watan da ta gabata
  • Majalisar ta tabbatar da nadin Amidu Raheem da Fasuwa Abayomi a matsayin kwamishinoni a hukumar NPC
  • Sanatocin sun ta tabbatar da nadin ne a yau Laraba 6 ga watan Maris a Abuja bayan Shugaba Tinubu ya tura bukatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Amidu Raheem da Fasuwa Abayomi a matsayin kwamishinoni a hukumar NPC.

Wannan tabbatarwar na zuwa ne bayan rahoton da kwamitin Majalisar ta kan kidaya ta gabatar a Majalisar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya amince a gaggauta raba wa mazauna Abuja kayan abinci

Sanatoci sun amince da muhimmiyar butakar Tinubu a yayin zamansu a yau
Majalisa ta amince da nadin Raheem da Fasuwa a matsayin kwamishinoni a NPC. Hoto: Godswill Akpabio, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wace bukatar Tinubu majalisar ta amince da ita?

Majalisar ta tabbatar da nadin ne a yau Laraba 6 ga watan Maris a Abuja bayan Shugaba Tinubu ya tura bukatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, a watan da ta gabata ne Tinubu ya tura bukatar inda shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya karanto.

Raheem wanda ya fito daga jihar Osun ya kasance malamin jami'a wanda shi ne shugaban tsangayar gudanarwa a Jami’ar Fountain da ke Osogbo.

Ya kasance tsohon mamban Majalisar jihar da ke wakiltar mazabar Iwo a Majalisar jihar Osun a shekarar 1992.

Ya kuma rike kwamishinan albarkatun ruwa da kuma makamashi karkashin mulkin tsohon gwamna Gboyega Oyetola, rahoton Tori News.

Yayin da Fasuwa shi kuma ya rike shugaban kwamitin ayyuka a Majalisar jihar Ogun wanda ya shahara a siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya yi muhimman nade-nade a kananan hukumomin jiharsa

Majalisa ta shiga duhu

Har ila yau, Sanatoci sun kasance ciki duhu a jiya Talata 5 ga watan Maris inda suka jira kamfanin wutar lantarki na Abuja ya dawo da wutar lantarki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa majalisar dattawa ta shiga cikin duhu har sai da aka dawo wutar.

An shawarci Tinubu kan tsadar rayuwa

A baya, mun ruwaito muku cewa Oba na Iwoland, Oba Abdulrosheed Akanbi ya bai wa Shugaba Tinubu shawara kan tsadar kayayyaki.

Akanbi ya ce ya kamata Tinubu ya kafa hukumar kayyade kayayyakin masarufi domin dakile matsalar da ake ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar kayayyaki wanda ya birkita ‘yan kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel