Majalisar Dattawa Ta Amince da Wani Muhimmin Nadin da Shugaba Tinubu Ya Yi

Majalisar Dattawa Ta Amince da Wani Muhimmin Nadin da Shugaba Tinubu Ya Yi

  • Majalisar dattawa ta amince da nadin Hafsat Bakari a matsayin shugabar hukumar NFIU kamar yadda Shugaba Tinubu ya buƙata
  • Bakari, wacce ta kasance lauya kuma kwararriya a harkar kudi za ta maye gurbin Midibbo Tukur wanda Tinubu ya cire shi daga mukamin a 2023
  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya nemi Bakari da ta zage damtse wajen inganta ayyukan hukumar kamar yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar dattijai a ranar Talata, ta tabbatar da nadin shugaba Bola Tinubu na Hafsat Bakari, a matsayin daraktar hukumar tattara bayanan laifukan kudi ta Najeriya (NFIU).

Majalisar ta tabbatar da nadi ne bayan karbar rahoton kwamitin majalisar kan yaki da cin hanci da rashawa wanda ya tantance Bakare.

Kara karanta wannan

Yayin da ake samun matsala a aure kan wasu dalilai a Kano, Majalisa ta dauki mataki don dakile haka

Tinubu ya nada Bakari a matsayin shugabar NFIU
A makon da ya gabata ne dai shugaba Tinubu ya nada Bakari a matsayin shugabar NFIU. Hoto: @NigFiu
Asali: Twitter

Kwamitin Sanata Udende ya tantance Bakari

Shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar dattawa, Sanata Emmanuel Menga Udende, ya mika rahoton ga majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattijai ta amince da shawarar kwamitin a lokacin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya nemi a kada kuri’a, The Nation ta ruwaito.

Akpabio ya taya Bakare murnar wannan mukami, ya kuma bukace ta da ta zage damtse wajen inganta ayyuka da daga darajar hukumar ta NFIU.

Bakari kwararriya ce kan harkokin kudi

A makon da ya gabata ne Premium Times ta ruwaito cewa Tinubu ya nada Bakari a matsayin shugabar NFIU har zuwa sa'in da majalisar dattawa za ta tabbatar da nadin na ta.

A nadin, Bakari za ta maye gurbin Modibbo Tukur wanda shugaba Tinubu ya sauke shi daga mukaminsa a watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

Bakari lauya ce kuma kwararriya kan harkokin kudi, wadda ta kwashe shekaru tana gogewa a fannin yaki da masu halasta kudaden haram, da yaki da masu rashawa.

Shugaba Tinubu ya kori Modibbo Tukur daga hukumar NFIU

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige Modibbo Hamman-Tukur daga mukamin shugaban hukumar tattara bayanan laifukan kudi (NFIU).

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa a Abuja, inda aka maye gurbinsa da Hafsat Bakari.

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Tinubu ya nemi Ms. Bakari da ta jajurce wajen yaki da shigo da kudin haram da dakile masu aikata laifuka da suka shafi kudi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel