Ana Shirin Azumi: Farashin Kwai Ya Yi Tashin Gauron Zabi Yayin da Manoma Suka Rufe Kasuwanci a Kano

Ana Shirin Azumi: Farashin Kwai Ya Yi Tashin Gauron Zabi Yayin da Manoma Suka Rufe Kasuwanci a Kano

  • Jama'a sun shiga damuwa saboda tsadar kaya da ake fama da shi gabannin fara azumin watan Ramadana
  • An rahoto cewa ana fama da karanci da tsadar kwai a jihar Kano, wanda abu ne da mutane ke yawan amfani da shi a watan azumi
  • Sai dai kuma, masu harkar kiwo su danganta tsadar kaji da kwai da ake fama da shi ga tashin farashin kayan hadin abincin kajin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Tashin farashin kwai da sauran abubuwan kiwo a jihar Kano ya jefa jama'a cikin damuwa, musamman a yanzu da Musulmai ke shirin fara azumi. Mutane kan bukaci kwai sosai a lokutan azumi.

An tattaro cewa a yanzu ana siyar da kwai kwaya daya kan N130 yayin da kiret din kwai ke kan N3,100.

Kara karanta wannan

An gano gawar 'yar jami'ar Najeriya a dakin kwananta

Farashin kwai ya yi tashin gauron zabi
Ana Shirin Azumi: Farashin Kwai Ya Yi Tashin Gauron Zabi Yayin da Manoma Suka Rufe Kasuwanci a Kano Hoto: Edwin Remsberg
Asali: Getty Images

Sai dai kuma, duk da tsadar sa, an fara samun karancin kwai a cikin garin, kuma hakan ya jefa mutane cikin damuwa yayin da sauran kayan kiwo suka fara fin karfin talaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene ke haddasa karancin kwai?

A cewar wani mazaunin garin, Abubakar Abdulsamad, dama akan samu karancin kwai idan lokacin azumin Ramadana ya fara kunno kai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa tsadar farashi da karancin kayan gona na faruwa da sakamakon boyewa da 'yan kasuwa ke yi.

Ya ce 'yan kasuwa na boye dan kwan da manoma ke fitarwa yanzu a jihar saboda su samu kazamin riba a lokacin Ramadana.

Wani mai kiwon kaji a jihar, Alhaji Isa Abba, ya ce yanzu ba zai iya ci gaba da harkar kiwo ba saboda tsadar kayan aikin ya fara wuce tunani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

A cewarsa, shi da wasu manoma da dama sun watsar da gonakinsu saboda abubuwa da dama da suka sa kasuwanci ya zamo mai wahala.

Ana fama da tsadar kayan hada abincin kaji

Sai dai kuma, shugaban kungiyar masu kiwon kaji na Najeriya, Dr Usman Gwarzo, ya alakanta karanci da tsadar kai kan tsadar kayan hada abincin kaji, tsadar kananan kaji, magunguna da sauransu.

Ya yi bayanin cewa tan na masara, wanda shine babban abin da ake amfani da shi wajen hada abincin kaji, wanda ake siyarwa N320,000 a watan Nuwamban bara, ya koma N550,000.

Legit Hausa ta tattauna da wani mai gidan gonar kaji don jin ta bakinsa.

Mallam Nuradeen mai kaji ya ce:

"Ba mu da abin cewa sai dai Alhamdulillah. Amma duk mai harkar kaji wala na kwai wala na ci karfin hali yake yi. Wallahi wasu lokutan na kan ji kamar na hakura da wannan sana'a amma idan na bar shi me zan yi?

Kara karanta wannan

Kano: Yadda wani mutum ya aurawa malaminsa yaransa mata 2 a lokaci guda, an maka shi gaban Hisbah

"Buhun abincin kaji masu kwai yanzu ya tasar ma N15,000 idan har mai inganci kake so. Kuma abincin shine zai sa su yi kwan ka ga mutum bai da dabara, idan kuma hadawa za ka yi da kanka, buhun dusa N16,000 ake siyarwa, kwanon masara N850 ya mutum zai yi.
"Gakiya ya kamata gwamnati ta duba don ina ganin ana gab da rasa masu yin wannan sana'a idan har ba a kawo mana tallafi ba.
"Idan ba a yi wasa ba yadda abubuwa ke tafiya sai an siyar da kiret din kawi N3500 zuwa azumi kuma ba laifinmu bane abubuwan samar da kwan ne suka yi tsada."

Masu gurasa sun yi zanga-zanga a Kano

A wani labarin, mun ji cewa wasu mata da ke sana'ar gurasa Kano, sun yi zanga-zanga domin nuna damuwarsu kan karin kudin fulawa.

Matan da suka yi tattaki a ranar Juma'a, sun ce tsadar fulawar ya jefa sana'arsu cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel