An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin da Tinubu Ya Ziyarci Babban Jagoran Kasar Yarbawa
- Daga cikin ayyukan baya-bayan nan da ya yi a jihar Ondo, Shugaban kasa Tinubu ya ziyarci gidan shugaban kungiyar Afenifere, Pa. Reuben Fasoranti
- An tsaurara matakan tsaro a kewaye da gidan Pa. Fasoranti da ke Akure, a ranar Laraba yayin da Shugaba Tinubu ya isa wajen don ganawar sirri
- Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya kai ziyarar ta’aziyya gidan Akeredolu a garin Owo, sannan ya hadu da matar marigayin, Betty Akeredolu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Akure, Jihar Ondo – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ka ziyara gidan shugaban kungiyar Afenifere, Reuben Fasoranti, a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.
An girke matakan tsaro masu tsauri a kewaye da gidan jagoran Yarbawan yayin da suka yi ganawa mai muhimmaci da Shugaban kasa Tinubu.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, wadanda sunayensu ke kan takardar tsaro ne kadai suka samu shiga harabar gidan jagoran na Afenifere, wanda ya goyi bayan Tinubu ya zama shugaban kasa a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu, wanda ya isa jihar a jirgi mai saukar ungulu, ya sauka ne a filin wasa na Akure, rukunin gidajen Ijapo, a ranar Laraba da misalign karfe 2:23 na rana.
Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa shugaban kasar ya isa gidan Fasoranti da misalin karfe 2:32 na rana.
Su wa suka yi wa Shugaba Tinubu rakiya?
Sauran manyan mutane da suka hallara a wajen sune Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo; Olu Falae, tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigon Afenifere.
Sauran sune Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Ogunlade; da tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko.
Shugaban kasar ya kuma kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
An ba 'yan Najeriya hakuri kan Tinubu
A wani labarin kuma, mun ji cewa Anthony Adefuye, mamba a majalisar ba da shawara kan harkokin mulki (GAC) a jam’iyyar APC reshen jihar Legas, ya bukaci ‘yan Nijeriya su ƙara hakuri da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Jigon jam'iyya mai mulkin ya kuma aminta da cewa ƴan Najeriya na fama da tsadar rayuwa da yunwa, amma a ganinsa ya kamata a kara ba Tinubu lokaci.
Asali: Legit.ng