Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar APC Don Yin Wasu Muhimman Abubuwa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Isa Jihar APC Don Yin Wasu Muhimman Abubuwa, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Akure, babban birnin jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Shugaban ƙasan wanda ya samu tarba daga gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, zai ziyarci iyalan tsohon gwamnan jihar, marigayi Rotimi Akeredolu
  • A yayin ziyarar ta sa a jihar Ondo a na sa ran shugaban ƙasan zai kai ziyarar ban girma ga shugaban ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere, a gidansa da ke birnin Akure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Akure, jihar Ondo - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Jirgin sojin saman Najeriya wanda yake ɗauke da shugaban ƙasan ya sauka a filin jirgin sama na Akure da misalin ƙarfe 11:35 na safiyar ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, cewar rahoton TVC News.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kama hanyar zuwa ta'aziyyar gwamnan APC da ya rasu, bayanai sun fito

Tinubu ya isa jihar Ondo
Shugaba Tinubu zai yi ta'aziyyar marigayi Akeredolu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da manyan jami'an gwamnati da fitattun ƴan siyasa ne suka tarbi shugaban ƙasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da fareti a tashar jirgin saman domin tarbar Shugaba Tinubu a jihar.

A lokacin da yake jihar, ana sa ran shugaban zai ziyarci fadar Olowo, Oba Gbadegesin Ogunoye da iyalan tsohon Gwamna Rotimi Akereodolu, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Ana kuma sa ran shugaban zai kai ziyarar ban girma ga shugaban ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, a gidansa dake birnin Akure.

Manufar ziyarar ta Shugaba Tinubu ita ce ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, waɗanda a halin yanzu suke a garin Owo.

An ayyana hutun kwana 2 a Ondo

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin jihar Ondo ta ayyana hutun kwana biyu a jihar saboda bikin jana'izar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tsohon gwamna ya nemo mafita ga 'yan Najeriya

Gwamnatin dai ta bayar da hutun ne domin karrama marigayi Akeredolu tarr da ba al'ummar jihar damar shiga cikin ayyukan jana'izarsa.

Shettima da Wasu Gwamnoni Sun Halarci Jana'izar Akeredolu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima, ya samu halartar jana'izar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Gwamnonin jihohin Legas da Ogun tare da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, na daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel