Mashawarcin Buhari Ya Ankarar da Tinubu, An Yi Mummunan Hasashe a Kan Naira
- Bismarck Rewane ya ce bin ‘yan canji da ake yi a kasuwa ba zai taimaka wajen sauko da kimar Dalar Amurka yadda ake tunani ba
- Masanin tattalin arzikin ya bada shawara ga bankin CBN ya narka kamar $500m a kasuwa, yana ganin wannan ne zai farfado da Naira
- Rewane ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin ba shugaban kasa shawara kan harkar tattalin arziki a mulkin Muhammadu Buhari
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Bismarck Rewane fitacce kuma kwararre ne a kan harkar tattalin arziki, ya yi wani kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A lokacin da ake fama da karyewar Naira, tashar Channels tayi hira da Bismarck Rewane domin jin ra’ayinsa kan halin da ake ciki.
Cafke 'yan canji zai karya Dala?
Masanin tattalin arziki ya soki yadda jami’an tsaro da hukumomin binciken rashin gaskiya suke wasan kura da ‘yan kasuwanin canji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Bismarck Rewane yana ganin cewa cafke ‘yan kasuwar canji da ke cinikin kudin ketare a bayan fage ba zai kawo gyara ba.
An rasa yadda Naira za ta tashi
Tun da bankin CBN ya daidaita kudin kasashen waje, Naira ta ke ta sunkuyawa. A bara masanin ya ce abubuwa za suyi sauki a 2024.
A sauran kasashe, Rewane yake cewa jami’an tsaro ba su shiga kasuwa suna damke ‘yan canji, ya ce hakan zai damalmala lamarin.
Idan ana so Naira ta mike, masanin ya ce CBN tana bukatar ta saki daloli a kasuwa.
Abin da zai farfado Naira a kasuwa
"A kyale abubuwa su daidaita, ainihin darajar Naira za ta fito. Wannan duk abin da na ke kira karkataccen zafin naman jami’an tsaro."
"Idan babban bankin Najeriya a yau ya saki $500m a kasuwa, duk ‘yan canjin za su koma gida domin babu wanda zai yi masu ciniki."
- Bismack Rewane
IMF ta ce Naira za ta rasa 35% a kimarta
Hukumar IMF mai bada lamuni a duniya tayi hasashen Naira za ta karye da kusan 35% a shekarar nan ta yadda $1 za ta kai N2, 081.
Gwamnatin tarayya na sa ran a samu sauki a kasuwar canji, a iya saida dala a N800. Rahoton IMF ya nuna kaya za su kara tsada da 44%.
Ba za a fasa karya Naira a kan Dala ba
Ganin Dala tana neman tabo N2, 000 wasu sun bada shawarara a sake duba batun sakin Naira a kasuwa domin ta nemo kan ta farashi.
Kaya sun kara tsada sannan rayuwa ta tsananta bayan cire tallafin man fetur, Bola Tinubu ya ce gyara ake yi kuma za a ga tasirinsa a gaba.
Asali: Legit.ng