Yadda wata mata ta yanke azzakarin mijin ta don yana bin matan banza a waje
Wani labari da muka samu daga majiyar mu yana tabbatar mana ne da yadda wata mata mai tsananin kishe ta sa wukar sarkin fawa ta gullewa mijin ta azzakari saboda yana neman matan banza a waje.
Matar da mijin wadanda ke zaune a garin Bangkok na kasar Thailand an ruwaito cewa ta yankewa mijin nata wannan danyen hukuncin ne bayan da ta gaji da halayyar 'yan awakin na sa.
KU KARANTA: Tsaffin gwamnoni 13 da Buhari ke shirin kwacewa kadarori
Legit.ng ta samu cewa makwaftan su ne dai suka ji ihun mai gidan na ta Siripan Sanusan mai shekaru 40 a duniya yana neman agaji kafin daga bisani su ruga da shi zuwa asibi.
Tuni dai 'yan sandan kasar suka damke matar Karuna Sanusan mai shekaru 24 a duniya bayan ta ansa aikata laifin.
A wani labarin kuma, Kotun duniya ta kasa-da-kasa dake a birnin Hague, a kasar Netherlands ta bayyana cewa kawo yanzu ta samu takardun korafi akalla 131 daga jama'a daban daban a Najeriya game da gazawar gwamnatin shugaba Buhari a fannin tsaro.
Wannan alkaluman dai sun fito ne daga kotun ta duniya inda ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton su na kwana-kwanan nan na binciken da suka yi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng