Tinubu Yana Bakin Kokarinsa, Ana Yunwa a Sauran Kasashen Waje Inji Sanatan APC

Tinubu Yana Bakin Kokarinsa, Ana Yunwa a Sauran Kasashen Waje Inji Sanatan APC

  • Sanatan Borno ta Kudu ya yi magana a kan matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta a karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu
  • Muhammad Ali Ndume ya ce har a sauran kasashe ana cikin matsi, yake cewa gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kawo gyara
  • Sanata Ndume ya lissafo hobbasan da Tinubu ya yi bayan cire tallafin fetur, a cewarsa dole kowa sai ya taka rawar gani a kasar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisa ya yi magana game da halin tattalin arzikin da kasa ke ciki.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya yi hira da tashar Channels a makon nan, a nan ya yi ikirarin akwai isasshen abincin da za a ci.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Tinubu
Ali Ndume ya kare Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Akwai abinci, Daloli ne babu a Najeriya

Duk da yadda ake kukan yunwa da tashin farashin abinci, Sanatan na kudancin Borno yana ganin ba abinci ne matsalar kasar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Inda gizo ke sakar a cewar ‘dan majalisar na APC mai rinjaye shi ne karancin kudin waje, Ndume ya koka da wannan a gidan talabijin.

A yanzu Dalar Amurka tayi mummunan tashin da ba a taba gani a tarihin Najeriya ba, duk da an fara samun sauki daga jiya Laraba.

Matsalar tattali ya kai kasashen ketare

Da aka zanta da Sanatan, ya bada uzurin cewa kasashen duniya da yawa suna fuskantar kalubalen tattalin musamman na abinci.

Rigimar Rasha da Ukraine da yakin Israila da mutanen kasar Falasdina sun taimaka wajen kawo matsala a kasashe a cewar Ali Ndume.

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

Sanata ya ce sai an taimakawa Tinubu

Bayan nan, Ndume ya ce lamarin ya fi karfin a bar shi a hannun shugaban kasa kadai, ya roki mutane su kawo shawarwarinsu.

‘Dan siyasar ya wanke Bola Tinubu, yana jero matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo sauki bayan cire tallafin fetur.

Daga ciki akwai rabon tallafi da shirin bada abinci ga wadanda ba su da hali.

Ndume ya yi ikirarin sauran ‘yan takara sun yarda za su cire tsarin tallafin fetur kuma ‘yan Najeriya sun yi maraba da aka yi hakan.

Majalisa za ta kawo kudrin katin sayen abinci

Kamar yadda muka rahoto a cikin shawarar wani masanin tattalin arziki, Ali Ndume ya fito da kudirin da zai kawo kati na sayen abinci.

Idan talaka ya mallaki wannan kati, zai iya amfani da shi a kasuwa domin ya saye kayan abinci a maimakon gwamnati ta saki kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel