Za a Komawa Karfin Bindiga Domin Sauko da Farashin Dala Ganin An Tsinci $1 a N1800

Za a Komawa Karfin Bindiga Domin Sauko da Farashin Dala Ganin An Tsinci $1 a N1800

  • Mai ba shugaban kasa shawarar tsaro zai taimakawa bankin CBN domin ganin an hana Dalar Amurka tashin babu gaira babu dalili
  • Wata sanarwa ta fito daga ONSA cewa jami’an tsaro za su kama wadanda ake zargi suna jawo hauhawar farashi a kasuwar canji
  • Jawabin Zakari Mijinyawa ya nuna za a cafke masu laifi kuma a hukunta su domin a rika samun ciniki cikin tsabta da gaskiya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro ya fitar da sanarwar cewa zai hada kai da babban bankin CBN.

A wani jawabi da ya fito daga bakin Zakari U. Mijinyawa, ofishin ya ce za a fara kama wadanda suke jawo farashin Dala yana tashi sama.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

Dala.
Tashin Dala ya jawo NSA zai shiga BDC Hoto: @NuhuRibadu/Getty Images
Asali: Twitter

A ranar Talata, Premium Times ta fitar da cikakken jawabin Malam Mijinyawa wanda shi ne shugaban sashen sadarwa a ofishin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NSA zai hana wasa da farashin Dala

Jawabin ya nuna an fito da yunkurin ne domin kare kasuwar canjin kudin kasashen waje kuma a hana jawo tangal-tangal a farashi.

Mai ba shugaban Najeriya shawara ta fuskar tsaron ya yabi matakan da bankin CBN yake bi domin ganin daidaita kasuwar canjin kudi.

Duk da haka, ana maganar $1 ta kusa N1900 a kasuwar canji, wanda hakan ya yi sanadiyyar tashin farashin mafi yawancin kaya.

"Ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro (ONSA) da bankin CBN za su hada-kai domin yakar kalubalen da tattalin arzikin kasa yake fuskanta."
"Domin a shawo matsalar tangal-tangal a farashi, idan za a tuna CBN ya kawo dabarun samar da kudi a kasuwar canji,"

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

"Daga ciki an daidaita farashin kudin waje, an biya bashin kudin ketare da ake bi, an fito da dabarun aikin ‘yan canji da bankuna"

- ONSA

An gaza hana farashin Dala tashi a BDC

A jawabin, an kawo batun yadda EFCC ta samar da jami’ai 7, 000 da za suyi maganin wadanda suke jawo Dala ta na kara tsada a kasuwa.

Duk da hobbasan da hukumar EFCC tayi, Dala ba ta fasa tashi ba don haka NSA ya tashi-tsaye domin a bunkasa tattalin arzikin kasar.

Dala: NSA zai hada-kai da jami'an tsaro

Wannan karo ofishin NSA zai hada karfi da karfe da bankin CBN, dakarun ‘yan sanda, jami’an kwatsam da ma'aikatan hukumar NFIU.

Zakari U. Mijinyawa ya ce rundunar hadin-gwiwar za su rika bincike domin kama wadanda ake zargi da laifi, sai a dauki mataki a kan su.

Usman Bugaje ya soki Bola Tinubu

A wata hira da aka yi da shi, ana da labari Usman Bugaje ya ce kowa ya gano Bola Tinubu bai da mafita game da matsalolin Najeriya.

Dr. Bugaje ya zargi Bola Tinubu da cire tallafin tetur ba tare da wani shirin magance halin tsadar rayuwa da kuncin da za a shiga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel