Masanin Tattalin Arziki Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru da Najeriya a Shekarar 2024

Masanin Tattalin Arziki Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru da Najeriya a Shekarar 2024

  • Bismarck Rewane yana cikin wadanda su ka tabbatar da abubuwa za su yi sauki a shekarar 2024 da za a shiga
  • Kaya sun kara tsada sannan Naira ta karye sosai, masanin tattalin arzikin yana ganin ba za a cigaba a haka ba
  • Rewane ya yi hasashen cewa Naira za ta farfado yayin da karyewar Dala za tayi sanadiyyar saukar farashi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bismarck Rewane yana cikin kwararru da ake ji da su a duk Najeriya a bangaren tattalin arziki, ya yi hasashe a kan 2024.

A makon nan The Cable ta rahoto Bismarck Rewane yana cewa ana sa ran darajar Naira za ta farfado, a samu sauki a kasuwar canji.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Bismarck Rewane
Bismarck Rewane ya yi hasahen tattalin arziki Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Hasashen Bismarck Rewane a kan tattali

Idan kimar Naira ta karu a kan kudin ketare, masanin ya ce tsadar kaya zai yi sauki. Gidan jaridar AbokiFX ta fitar da wannan labari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kamfanin na Financial Derivatives ya bayyana haka ne a wajen wani taro da Parthian Partners ta shirya a garin Legas.

An yi taron ne domin tattaunawa game da yadda ake tunanin abubuwa za su kasance ta fuskar tattalin arziki a shekarar badi.

Halin da tattalin arziki ya shiga a 2023

Bismarck Rewane ya ce a shekarar nan, darajar Naira ta karye da 26%, Dala ta kai N1050.

Baya ga tsadar kaya da hukumar NBS ta tabbatar, sai da aka saida Dalar Amurka a kan N1, 099, abin da ba a taba gani a bankuna ba.

An samu karin tsadan dizil zuwa 34.01% da lita ta zarce N1000 a bana, sannan fetur ya zarce N630 (karin fiye da 230%) a shekarar nan.

Kara karanta wannan

To fah: Fitaccen malami ya ayyana shiga tseren takarar gwamna a jihar PDP, ya faɗi dalili

Kudin da yake yawo a gari kuwa ya karu zuwa 36%. Duk da wahalar kudi da ake yi, Rewane ya ce N67.18tr su kayi yawo a Satumba.

Ra’ayin masanin ya zo daidai da na gwamnan bankin CBN, Yemi Cordoso wanda ya yi alkawarin za a samu saukin tsadar kaya a 2024.

Bola Tinubu ya tashi kudin fetur

A ranar da Shugaba Bola Tinubu ya shiga ofis, ya cire tallafin man fetur kuma alkaluma sun nuna tsadar kaya ya kai 28.2% a yau.

Bola Tinubu ya ce hakan ya zama dole ne saboda halin tattalin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel