Murna Ta Barke Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Siyar da Shinkafa Kan Farashi Mai Rahusa Ga Talakawa

Murna Ta Barke Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Siyar da Shinkafa Kan Farashi Mai Rahusa Ga Talakawa

  • Dattawa da masu ƙaramin karfi zasu samu shinkafa kyauta yayin da Gwamna Abiodun ya fara yunkirin ragewa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa a Ogun
  • Dapo Abiodun ya tabbatar da haka a wata sanarwa kuma ya ce mazauna Ogun zasu sayi shinkafa a kan asalin farashinta kafin tashin dala
  • Wannan yunƙurin gwamnan na jam'iyyar APC zai ci gaba har zuwa lokacin da za a warware matsalar da ta taso a kasuwar canjin kuɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Yayin da ake fama da matsin tattalin arziki, gwamnatin jihar Ogun ta siyo tirelolin buhunan shinkafa domin siyarwa talakawan jihar a farashi mai rahusa.

A cewar gwamnatin jihar, ta ɗauki wannan matakin ne ba don komai ba sai don magance hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mutuwar mutum hannun jami'an tsaro ya sa an nemi Gwamna ya tashi tsaye

Gwamna Abiodun ya rage farashin shinkafa.
Murna Ta Barke Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Siyar da Shinkafa Kan Farashi Mai Rahusa Hoto: @DabiodunMFR
Asali: Twitter

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ne ya tabbatar da haka a taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024 a Abeokuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jerin saƙonnin da ya wallafa a manhajar X watau Twitter, Gwamna Abiodun ya ce zai saka tallafi a shinkafa kuma za a siyarwa mutane a farashi mai sauƙi.

Kan wane farashi gwamnan zai siyar da Shinkafa?

Abiodun ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta siyarwa da al'ummar jihar Ogun buhunan shinkafa a kan asalin farashinta gabanin hauhawar da aka samu bayan faɗuwar darajar Naira.

Wannan wani ɓangare ne na tallafin N5bn da Gwamna Abiodun ya lashi takobin sanyawa a tattalin arzikin jihar Ogun domin magance tsadar rayuwar da mutane suka shiga.

A sanarwan da ya wallafa, Abiodun ya ce:

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta ɗauki mataki kan tsohon gwamnan Arewa da ake zargi, ta kafa sharuɗda

"Domin tabbatar da an yi adalci wajen rabon tallafin, mun yanke bai wa tsofaffi da masu ƙaramin karfi shinkafar a kyauta yayin da saura zasu siya a farashin asali kafin tashin dala.
"Wannan zai bamu damar ci gaba da wannan aiki daga nan har zuwa lokacin da za a warware matsalar dala, yana da kyau kowa ya sani wannan kalubalen na wani ɗan lokaci ne."

Yaushe dala zata faɗi warwas a Najeriya?

A wani rahoton kuma Dapo Abiodun ya tabbatar da cewa nan da wani taƙaitaccen lokaci dala zata rikito ta faɗo ƙasa yayin darajar Naira za ta dawo a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa ya samu wannan tabbaci ne a wurin ganawar da gwamnoni suka yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel