An Kai Karar Sunusi Lamido Ga Tinubu Kan Bala’in da Ke Tunkarar Kano Kan Masarautu, an Fadi Dalili

An Kai Karar Sunusi Lamido Ga Tinubu Kan Bala’in da Ke Tunkarar Kano Kan Masarautu, an Fadi Dalili

  • Cibiyar kare dan Adam a Najeriya (SHAC) ta tura gargadi ga hukumomi kan matsalar da ke neman faruwa a Kano kan masarautu
  • Hukumar ta ce kalaman tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido da mukarrabansa ka iya jefa jihar a wani yanayin rashin zaman lafiya
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kiran a sauya fasalin tsarin masarautun da aka kirkira da kuma mayar da Sunusi kujerarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Cibiyar Kare dan Adam ta SHAC ta nuna damuwa kan yadda tsohon Sarkin Kano da makarrabansa ke son tada zaune tsaye a jihar.

Kungiyar ta na zargin akwai wani shirin da ke nuna ana son kawo rashin zaman lafiya kan kalaman da wasu na jikin Lamido ke yi.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

An kai karar Sunusi ga Tinubu kan matsalar masarautun Kano
Wata cibiya a Najeriya ta kai karar Sunusi ga Shugaba Tinubu. Hoto: Sunusi Lamido, Bola Tinubu, SHAC.
Asali: Facebook

Mene ake zargin Sunusi da yi?

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da ta rubuta wa Shugaba Tinubu a makon da ya gabata, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Acikin wasikar, kungiyar ta bukaci a takawa Sunusi da mukarrabansa birki kan irin wasu kalamai da ke fitowa daga gare su.

Babban darktan kungiyar, Attah Musa ya yi zargin ana neman sake duba tsarin masarautun jihar ganin yadda siyasar jihar ke tafiya a yanzu.

Attah ya ce hakan ka iya jawo rashin zaman lafiya a jihar musamman a halin da ake ciki yanzu a jihar musamman a siyasance, cewar Daily Trust.

Sanarwar ta ce:

“Muna godiya ga Shugaba Tinubu kan kokarinsa na shawo kan matsalolin Najeriya da ta ke fama da su.
“Muna son yin amfani da wannan dama don sanar da kai kan wasu ayyukan tsohon Sarki, Sunusi Lamido da za su iya jawo matsala a Kano.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

“An sani cewar Lamido su na da alaka da gwamnatin Kano a yanzu wanda ya ke jawo wasu kalamai daga wasu bangarori da ka iya rusa zaman lafiyar jihar.”

Sanarwar ta kara da cewa:

“Shugaba Tinubu ya kamata ka sani wasu kalamai da Lamido ke yi da mukarrabansa za su iya tarwatsa zaman lafiyar jihar.
“Hakan bai rasa nasara da maganar masarautun Kano wanda idan ba a bi a hankali ba zai iya jefa jihar a cikin mummunan rikici.”

Kungiya ta gargadi Majalisa kan Sunusi

Kun ji cewa wata kungiyar a jihar Kano ta gargadi Majalisar jihar kan amincewa da sake duba masarautun jihar.

Kungiyar mai suna Masarautar Bichi ta ce idan ba a bi a hankali ba taba masarautun zai jawo babbar matsala da rashin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel