Sanatan Arewa Ya Kawo Dabarar da Talaka Zai Iya Mallakar Abinci Babu Ko Sisi

Sanatan Arewa Ya Kawo Dabarar da Talaka Zai Iya Mallakar Abinci Babu Ko Sisi

  • A maimakon a rika bada kudin da za a karkatar, Muhammadi Ali Ndume ya zo da tsarin da marasa hali za su iya yin cefanen gida
  • Kudiri ya je majalisa domin a ba gwamnatin tarayya ikon raba katin da za a iya sayen abinci da shi yayin da kaya suka yi tsada
  • Kansiloli da shugabannin kananan hukomomi za su tantance talakawan mazabunsu da za a ba katin nan na musamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Muhammad Ali Ndume da wasu abokan aikinsa da ke majalisa sun kawo kudirin da ake sa rai zai taimaka a wajen rage yunwa.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce suna kokarin kirkiro da katin sayen abinci.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zakzaky yana magana kan harsashi 38 da likitoci suka gano a kwakwalwarsa ya yadu

Ali Ndume
Sanata Ali Ndume ya kawo kudirin rage yunwa a majalisa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Kudirin da aka shigar majalisa

Idan kudirin ya zama doka bayan amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya hau mulki a bara, zai saukaka wajen samun abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a fito da wannan kati ne domin kananan ma’aikata wanda albashinsu ba zai isa su saye kayan abinci ba saboda hauhawar farashi a yau.

Duk wanda ya samu katin zai je kasuwa ya samu dillalai, sai su ba shi abincin daidai kudinsa, daga baya sai a biya ‘yan kasuwan a bankuna.

Tarihin katin sayen abinci

Sanatan na Kudancin Borno ya ce a Amurka aka fara kirkiro wannan tsari a 1939, yana ganin tsarin zai iya aiki a karon farko a Najeriya.

‘Dan majalisar yake cewa an jarraba tsarin a jihar Legas a shekarun baya, kuma an amfana, hakan zai fi a rika raba kudi a gidajen talakawa.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan wasan kwallon kafa 10 da aka taba yankewa hukuncin dauri da laifukan da suka aikata

Ya za ayi da rashin gaskiya?

Ana zargin rashin gaskiya yana shiga tsare-tsaren da ake kawowa na rabawa mutane kudi, saboda haka Sanatan ya kawo dabarar nan.

Ndume yana da tsoron cewa barna tana shiga tallafi ne musamman wajen tattaro sunayen wadanda za su ci moriya ta hannun kwararru.

A wannan tsari da yake majalisar dattawa, kansiloli da shugabannin kananan hukomomi za a ba alhakin yi wa marasa hali rajista.

Da zarar mutum ya yi rajista, sai a tantance gaskiyar karfin tattalin arzikinsa, idan ya cancanta zai a ba shi kati da zai rika amfani da shi.

Za a rika karbar abinci ne duk wata kuma a wannan lokaci ‘yan kasuwa za su je banki domin a biya su duk kudin kayan da suka saida.

Masanin tattali ya yabi tsarin

A matsayinsa na malami a sashen tsimi da ilmin tattalin arziki a jami’ar ABU Zariya, Usman Bello ya shaidawa Legit muhimmancin tsarin.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Dr. Usman Bello ya fada mana za a iya amfani da lambar NIN wajen zakulo wadanda za a ba katin, hakan zai fi kyau a kan a yi ta raba kudi.

Masanin ya ce rabon kudi barkatai yana da illa kuma ba dole ya yi tasirin da ake so ba.

Malamin yake cewa fito da katin zai sa wadanda suka boye abinci su fito da shi domin gwamnati za ta saye buhuna da Daraja sosai.

Haka zalika Dr. Bello ya na ganin tsarin zai zaburar da mutane suyi noma sosai tun da ba za suyi asara ba idan gwamnati ta saye kayansu.

“Ana yunwa duk duniya” - Sanata Ndume

Ana da labari cewa Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce kasashe da yawa sun shiga matsi yadda ake ciki a Najeriya a irin wannan lokaci.

Sanatan na Borno yana ganin sai an taimakai Bola Tinubu da shawarwari, shi ya fadi matakan da aka dauka kuma ya bada gudumuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel