Jerin ’Yan Wasan Kwallon Kafa 10 da Aka Taba Yankewa Hukuncin Dauri da Laifukan da Suka Aikata

Jerin ’Yan Wasan Kwallon Kafa 10 da Aka Taba Yankewa Hukuncin Dauri da Laifukan da Suka Aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A tsawon lokaci, an samu wasu 'yan wasan kwallon kafa da aikata laifuka daban-daban a wajen wajen filin wasa kuma an yanke musu hukunci bisa doka.

Sun yi zaman gidan yari a matsayin hujjar cewa, duk da tauraruwarsu tana haskawa a kwallon kafa, ba su fi karfin doka ba idan suka aika wani laifi da ya sabawa dokar.

Legit Hausa ta tattara jerin sunayen ’yan kwallon kafa goma da suka yi zaman gidan yari, da kuma laifukan da suka aikata, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

Jerin 'yan wasan kwallon kafa da suka je gidan yari
Akwai 'yan wasan kwallon kafa da suka aikata laifuka daban-daban da ya kaisu gidan yari. Hoto: @COYHorns_com, @10Ronaldinho
Asali: Twitter

’Yan kwallon da suka yi zaman gidan yari

1. Nizar Trabelsi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya kawo dabarar da talaka zai mallaki buhun abinci babu ko sisi

Trabelsi ya buga wa Fortuna Dusseldorf wasa na tsawon kaka daya a lokacin yana Jamus.

An kama Trabelsi jim kadan bayan fara wasansa saboda alakarsa da Al-Qa’ida. An samu Trabelsi da laifin shirya harin da aka kaiwa sojojin Amurka a sansanin sojin sama na Belgium.

Bugu da kari, ana kyautata zaton shi ne ya shirya ta'addancin da ya shafi ofishin jakadanci Paris, bayan da aka ba shi mukamin dan kunar bakin wake da zai kai harin.

An yankewa Trabelsi hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a shekara ta 2003.

2. Lee Hughes

Wata rana da yamma yana tuki, tsohon dan wasan West Bromwich Albion, Hughes ya yi karo da Mercedes dinsa da wata motar, inda ya kashe wanda ke cikin dayar motar.

Mafi muni ma, akwai jita-jitar cewa Hughes yana cikin maye ne ya ke tuƙin. Hughes ya mika kansa ga 'yan sanda a washegarin ranar inda aka bayar da belinsa.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

A shekara ta 2004 ne aka samu Hughes da laifin kashe wani ta hanyar tukin ganganci, ya samu hukuncin zaman gidan yari na shekaru shida tare da dakatar da shi daga tuki na shekaru goma.

3. Joey Barton

An fara yanke wa Barton hukunci bisa zargin cin zarafi a lokacin da kade wani mai tafiya a ƙasa a Liverpool. An tura shi zaman gidan yari na 77.

Duk da haka, a ranar 1 ga Yuli, 2008, an dakatar da Barton na watanni hudu bayan farmakar tsohon abokin wasansa na Manchester City, Ousame Dobo har ya ji masa rauni.

4. Ronaldinho

A wata ziya da ya kai Paraguay, an kama Ronaldinho da dan uwansa Roberto de Assis bisa laifin amfani da takardar fasfo na bogi.

A shekarar 2020, sun amsa laifinsu a gaban kotu, inda aka rage musu hukuncin daga shekaru biyar zuwa watanni biyar tare da biyan tarar dala 200,000 (£167,000).

Kara karanta wannan

Jami’an EFCC sun kai samame wurin ‘yan canji a Kano, Abuja da Oyo akan wani dalili 1 tak

5. Adam Johnson

Johnson yana daya daga cikin kwararrun 'yan wasan kwallon kafa da aka yankewa hukuncin dauri saboda laifin haike wa yara.

An yankewa tsohon dan wasan Manchester City da Sunderland hukunci a shekarar 2016. Sunderland ta kore shi saboda haike wa wata yarinya ‘yar shekara 15.

6. George Best

Best, ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa na Manchester United na tsawon lokaci, yana da salon mummunar rayuwa wanda ya cutar rayuwarsa.

Best rikakken mashayi ne, wanda akai-akai yake shafar harkar kwallon kafarsa. Best ya fara fuskantar sauyin rayuwa mafi muni a cikin shekarar 1984.

An aika Best zuwa gidan yari bayan kama shi da laifin tuki cikin maye, da cin zarafin dan sanda, da kuma kasa cika sharuddan beli.

7. Duncan Ferguson

Ferguson yana da matsaloli da yawa, ciki har da zarge-zargen cin zarfi guda hudu, uku daga ciki aka warware su da biyan tara.

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

Babban laifin da ya aikata, shine lokacin da Ferguson ya gwara kansa da na mai tsaron bayan Raith Rovers, wato John McStay a lokacin da yake bugawa Rangers wasa a 1994.

An yanke wa Ferguson hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda laifin gwara kai, duk da cewa lamarin ya faru a filin wasa.

8. Rene Higuita

A shekara ta 1993 ne aka fara daure Higuita a gidan yari saboda hannu a garkuwa da shahararren dillalin muggan kwayoyi na kasar Colombia Pablo Escobar.

Duk da yake aikin Higuita shine kawai ya ba da kuɗin fansa, amma an biya shi wannan aikin, kuma hakan ya saba wa dokar Colombia ta amfana da harkallar satar mutane.

9. Marlon King

An daure tsohon dan wasan Birmingham da Wigan na tsawon watanni 18 a shekara ta 2009 saboda laifin cin zarafin wata mata da kuma karya mata hanci.

A cikin shekarar 2014, an saka masa takunkumin yin tuƙi na shekaru uku bayan amsa laifin tuƙin ganganci a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Wasan karshe na AFCON: Gaskiyar batu kan bidiyon da ke zargin golan Ivory Coast da sanya guraye

10. Tony Adams

Tsohon dan wasan baya na Arsenal ya sha fama da matsalar shaye-shaye a tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa.

A cikin watan Mayu, 1990, ya farfasa motarsa ​​a bango kusa da gidansa, kuma bayan gwaje-gwaje, an gano cewa ya ninka iyakar gudun ka'ida sau 27.

An yanke wa Adams hukuncin daurin watanni hudu a watan Disamba, amma an sake shi a farkon watan Fabrairu.

Kotu ta daure Dani Alves, tsohon dan wasan Barcelona

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata kotu a Andalus ta yanke wa Dani Alves, tsohon dan wasan Barcelona hukuncin zaman gidan yari na shekara hudu.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da ta sami Dani Alves da laifin haikewa wata mata, kuma an umarce shi ya biya diyyar Yuro dubu 150.

Asali: Legit.ng

Online view pixel