Wani Mutum Ya Gayyaci Abokinsa Zuwa Dubai, Ya Kashe Wayarsa Bayan Ya Isa Kasar
- Wani mutum ya bada labarin wahalhalun da ya fuskanta lokacin da ya fara zuwa hadaddiyar daular Larabawa, wato Dubai
- A wani labari mai sa hawaye da ya bayar a TikTok, mutumin ya ce ya je kasar Dubai da nufin zama tare da daya daga cikin abokansa
- Amma ya ce lokacin da ya sauka a filin jirgin, abokin da yake fatan zama da shi ya kashe wayoyinsa, sannan ya makale a wajen
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani mutum da ya yi tattaki zuwa Dubai, hadaddiyar daular Larabawa a 2010 ya bada labarin yadda ya makale a kasar.
A cikin labarin da @otunbatgold ya yada, mutumin ya ce abokinsa, wanda ke zaune a Dubai, ya fada masa cewa akwai kudi sosai a kasar.
Don haka sai ya yanke shawarar komawa Dubai domin shima ya tara abin duniya kamar abokinsa. Ya yi fatan zama tare da abokin nasa, amma dai sai hakan ya zamo kuskuren da ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mutum ya makale a kasar Dubai
Da ya isa daular Larabawan sannan ya kira lambar wayar abokinsa a filin jirgin sama, Otunba ya ce abokin nasa ya yi masa layar zana.
Ya ce wayar abokin nasa ta kasance a kashe, wato kenan zai ta yawo a titi ba tare da wajen da zai sanya hakarkarinsa ba.
Ya ce sa'arsa daya yana da wani abokin, amma dai abubuwa basu zo cikin sauki ba saboda akasin da aka samu tun da farko.
Masu amfani da TikTok da dama sun cika da mamakin abin da zai sa mutum ya yi wa abokinsa irin wannan abu. Wasu sun ce irin haka ya taba faruwa da su a baya.
Jama'a sun yi martani
@EverLasting ta tambaya:
"Me yasa mutane suke kashe waya idan abokansu suka isa filin jirgin sama?"
@Gbayor ya yi marytani:
"Inda kake zaune ma na da kyau. Wasu mutanen ma a tasahar mota suke kwana."
@dunni ta ce:
“Allah ba zai ba mu kunya ba.”
@Obehi ya ce:
“Labarinmu iri daya ‘dan uwa. Dubai ba na masu rauni bane. Wata daya nayi na gudo Najeriya. Nagode Allah yanzu ina Ingila kuma na gode zuwa yanzu. Ban cike tsammani ba.”
@Sirmido ya yi martani:
"Wannan sak nine a 2018."
Bature ya zo Afrika ya yi aure
A wani labari na daban, wani bature da ke aikin tuka jirgin sama ya baro duk matan da ke yankinsa inda ya garzayo nahiyar Afrika domin auren wata budurwa yar kauye a kasar Kenya.
Tuni aka sha shagalin bikinsu harma Allah ya albarkace su da haihuwar 'da.
Asali: Legit.ng