Matashi Ya Yi Cuku-Cukun Fita Daga Talauci, Ya Kera Katafaren Gida Na Alfarma da Siyan Mota

Matashi Ya Yi Cuku-Cukun Fita Daga Talauci, Ya Kera Katafaren Gida Na Alfarma da Siyan Mota

  • Wani matashi wanda ya taso a cikin talauci ya gina gidan kansa ya kuma ba da labarin yadda tafiyarsa ta kasance a cikin wani bidiyo
  • Bidiyon ya hasko yadda ya fara ba tare da komai ba illa yar babur da ya mallaka sannan ya yi ta fadi tashi har ya kai matakin da yake a yanzu
  • Ya kuma zaga da mutane cikin katafaren gidansa mai ban mamaki, wanda aka zuba kayan more rayuwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Bidiyon wani matashi da ya shawo kan talaucinsa tare da cimma mafarkinsa na gina katafaren gida nasa na kansa ya taba zukatan mutane da dama.

Bidiyon ya nuno sauyawar da ya yi na ban mamaki daga mai tuka babur da ke fama da rayuwa zuwa shahararren dan kasuwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka ‘sace’ mawaki da ƴan amshinsa a Abuja

Matashi ya kera katafaren gida
Matashi Ya Yi Cuku-Cukun Fita Daga Talauci, Ya Kera Katafaren Gida Na Alfarma da Siyan Mota Hoto": @worldxx01/TikTok
Asali: TikTok

Ya baje kolin hadadden gidansa, wanda ke tabbatar da kwazo da jajircewarsa a aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya nuno cikin gidan da aka kawata da kayan alatu, harda manyan kujerun alfarma, da hasken wuta ta ko'ina.

Labarinsa ya zaburar da mutane da dama akan kada su yanke kauna da cimma mafarkinsu tare da jajircewa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

Yungstar empire ya yi martani:

"Allah me ke faruwa da ni ne? Ni cokali ne?"

Ema _nation ya ce:

“@Worid don Allah kamar nawa ka kashe wajen gina gidan nan. Ina so na jajirce ne zuwa shekara mai zuwa."

Highest bee ya rubuta:

“Wani ya yi amfani da gidan nan jiya AJE.”

User4373262740652:

"Ina tayaka murna sosai daga dubai."

Ashanti m:

"Na tayaka murna dan uwa ba abu mai sauki bane."

Kara karanta wannan

Yar Najeriya ta gina dankareren gida a wata 7, ta yi bidiyo ta na tikar rawa don murna

Matshiya ta gina gidan dinki

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta bayyana tsantsar farin cikinta yayin da ta yi nasarar kammala aikin gidan dinkinta.

Matashiyar mai suna 'Celebrities Tailor' a TikTok, ta bayyana cewa tana matukar farin ciki da ganin abubuwa sun kammalu a gidan dinkin.

Ta ce shekarunta 20 kacal a duniya, amma ta zama shugaba da kanta a lokacin da take ganiyar kuruciya kuma ta cimma hakan ne cikin wata guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel