“Na Gaji da Kasar Nan”: Dirama Yayin da Yar Najeriya Ta Nemi Kwandastan Mota Ya Kai Ta Amurka

“Na Gaji da Kasar Nan”: Dirama Yayin da Yar Najeriya Ta Nemi Kwandastan Mota Ya Kai Ta Amurka

  • An sha yar dirama lokacin da wata budurwa yar Najeriya ta tsare motar haya sannan ta bukaci a kai ta kasar Amurka
  • A wani bidiyo mai ban dariya da ya haddasa cece-kuce a TikTok, matashiyar ta dage cewa ta gaji da Najeriya kuma tana so ta tafi waje
  • Kwandastan bas din ya shiga rudani amma ya fada ma matashiyar cewa motar zuwa Amurka N300 ne, wanda hakan ya sa sauran fasinjoji fashewa da dariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya yar Najeriya ta bukaci wata motar bas ta kai ta Amurka yayin da ta dage cewa ita ta gaji da kasar nan.

Wani bidiyo da ke yawo a TikTok ya nuno lokacin da matashiyar ta tsayar da motar bas sannan ta bukaci a tukata zuwa Amurka.

Kara karanta wannan

"Sun yi zaton damfara nake yi": Mai aiki a gidan mai ta dau wanka ta bayan aiki, bidiyon ya yadu

Budurwa ta nemi direban bas ya kai ta Amurka
“Na Gaji da Kasar Nan”: Dirama Yayin da Yar Najeriya Ta Nemi Kwandastan Mota Ya Kai Ta Amurka Hoto: TikTok/@reekyohk.
Asali: TikTok

Lokacin da ta sanar da kwandastan motar cewa Amurka take son zuwa a bas dinsa, matashin ya dan shiga rudu da farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar ta ce tana so ta fita waje sannan kuma cewa da ba za ta shiga motar ba idan da ta san ba Amurka zai je ba.

Sauran fasinjojin motar sun fashe da dariya bayan sun saurari bukatar budurwar mai ban dariya.

An yi wa bidiyon mai ban dariya wanda @reekyohk, ta yada take da:

"Na gaji da kasar nan."

Kalli bidiyon:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon

@sharoy laks ta ce:

"Wahala ya yi kamar Amurka, wata mata cewa ta yi zani Dubai."

@PABLOBETHEL ya ce:

"Yallabai ya kadu na sakan biyu. Wani Amurkan."

@mikaylaforson4 ya yi martani:

"Eii! Abun da kuke yi kenan sannan a sace ku. Wacce matsa ce ban taba gani ba?"

Kara karanta wannan

“Kada ka biya sadaki”: Budurwa ta fashe da kuka yayin da ta roki dan aikin Davido ya aureta a bidiyo

@iyke_da_first! ta ce:

"Na tuna lokacin da na yi nirin wannan zolayar a makarantar sakandare, dan keke ya kusa ji mani ciwo. Ban san dalilin da yasa yake fushi ba."

@Nelson2 ya yi martani:

"Yadda ta bata rai take cewa Amurka."

@JAC ya ce:

"Wannan hanyar na bani tsoro da rana balle kuma da daddare. Allah ya kare ku dukka."

Daddy Freeze ya shawarci maza

A wani labari na daban, Shararren mai fadi a ji a dandalin sada zumunta, Ifedayo Olarinde wanda aka fi sani da Daddy Freeze, ya ba maza wata shawara kan zamantakewa.

Sanannen mutumin ya saki wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya fada ma maza cewa su fara karbar kudade daga hannun matayensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel