Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa, Ya Ce Mafi Karancin Sadaki Yanzu Ya Koma N48,985 a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa, Ya Ce Mafi Karancin Sadaki Yanzu Ya Koma N48,985 a Najeriya

  • Addinin Islama ya tanadi komai bisa ka'ida a kan tsarin da babu cuta, kuma babu cutar da wani ta kowacce fuska
  • An sanar da samun sauyi a bangaren Sadaki, Diyyar, da ma kudaden da mutum zai mallaka har su kai a fitar musu da Zakkah
  • A duk lokacin da aka samu sauyi, addinin Islama kan zo da hanyoyin da za su zama maslaha ga al'umma ba tare da shigewa duhu ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Najeriya - A ranar Juma'a, 12 ga watan Dhul Hijjah Hijira 1444, wacce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2023, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar nisabin Zakkah, Sadaki da Diyyar rai.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal da gudanar da idin babbar Sallah da aka gudanar a ranar Laraba 10 ga watan Dhul Hijjah na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

An kuma: Za a saka wa 'yan Twitter takunkumi, an fadi adadin rubutun da za su ke gani a rana

A sanarwar da sarkin Musulmin ya fitar, wacce hukumar kula da ganin jinjirin wata ta yada a shafinta na Facebook, an bayyana adadin kudade ga kowane bangare.

Kudin sadaki ya tashi a Najeriya
Kudaden Najeriya da kowa ke amfani dasu | Hoto: Damilola Onafuwa/Bloomberg via Getty Images
Asali: Getty Images

Nisabin Zakkah, Haddin Sata da Sadaki, da kuma Diyyar rai

A cewar sanarwar, yanzu nisabin Zakkah ya koma N3,918,800, wanda aka kwatanta da darajar farashin kwal a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangaren haddin sata da kuma sadaki na auren mace, dole sai ya kai akalla N48,985 kafin ya cika ka'idar shari'a.

Abin da hakan ke nufi shine, ana yanke hannun barawo ne idan a shari'ance idan ya saci dukiyar da ta kai aalla N48,985.

Yadda batun sadaki yake a shari'ar Muslunci

Hakazalika, a shari'a dole mai neman aure ya ba da sadakin da bai yi kasa da N48,985 ba don cikar ka'idar daurin aure.

A bangaren Diyyar rai, ana daurawa wanda ya yi kisa biyan Diyya ne a kan kudi N195,940,000, duba da darajar kudade da ake dasu a yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

Wadannan na kadan daga cikin hanyoyin da addinin Islama ya tanada don yiwa kowa adalci a fannin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Yadda nisabi yake a shekarun baya

A shekarun da suka gabata, majalisar koli ta addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana nisabin karancin sadaki a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta samu zantawa da Sheikh Khamis Al-Misriy, limamin masallacin Abu Ubaidah Bn Jarrah dake bye-pass jihar Kaduna domin samun karin haske.

Kamar yadda malamin ya sanar, nisabi dai shine wani ma'auni da ake gwadawa domin a gane darajar kudi da inda ya kai. A musulunce kuwa ana kiran shi da kaso daya bisa hudu na dinari daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel