2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC

2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC

  • Babban malamin addinin musuluncin nan a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya zama dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar ADC
  • Shugaban ADC reshen Kano wanda ya tabbatar da haka, yace Malamin shi kadai ne ya siya fom din takarar kujerar
  • Shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Ralph Okay Nwosu ya bayyana cewa mutuncin malamin da amincinsa ne yasa suka mika masa tutar su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Fitaccen malamain nan na Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, ya zama dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam’iyyar Africa Democratic Congress (ADC), Solacebace ta rahoto.

An tattaro cewa Sheikh Khalil wanda ya zama dan takarar jam’iyyar bayan ya bayyana bai da abokin hamayya a wani taro da aka gudanar a ranar Lahadi, zai yi fafutukar babbar kujerar jihar ne tare da yan takarar sauran jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC
2023: Sheikh Ibrahim Khalil ya tabbata dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Aminiya ta rahoto cewa malamin ya sayi fom din takarar ne kan naira miliyan 10 sannan zai zama dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa kasancewar shi kadai ne ya sayi fom din kujerar.

Shugaban jam’iyyar ta ADC a jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungogo, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar ne da kan su suka yanke shawarar zuwa har Jihar Kano don kawo masa fom din saboda muhimmancinsa da na Jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ungogo ya ce:

“Duk sauran masu neman takara sukan je hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja ne don siyan fom, amma shi Sheikh Khalil bayan ya biya kudin, sai suka ce ya dawo za su kawo masa har gida.
“Hakan ne ya sa Shugaban jam’iyyar na kasa da Sakatarensa da kuma Mataimakin Shugaba na Shiyyar Arewa maso Yamma suka zo har Kano don gabatar masa da fom din.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

“Shugaban ya kuma yi amfani da bikin wajen rantsar da Shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar, karkashin Farfesa Kabiru Dandago."

Yayin da yake gabatarwa Sheik Khalil da fom din takarar gwamnan na ADC a Mumbayya House da ke Kano, shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Ralph Okay Nwosu ya ayyana cewa mutuncin malamin da amincinsa ne yasa suka mika masa tutar su.

Shugaban jam’iyyar wanda ya nanata gaskiya jam’iyyar kan gaskiya da mutunci, ya jadadda cewa cencantar Sheikh Khalil wanda da shine ADC ta dogara zai sa su kawo jihar Kano a zaben.

Ya bayar da tabbacin cewa ADC za ta nada mata a kaso 35 cikin 100 na mukaman siyasa sannan za ta karfafa matasa domin ganin sun cimma burinsu a rayuwa.

Shahararren Malamin Musulunci a Kano da wasu Manyan Farfesoshi 8 sun shiga jam'iyyar siyasa

A baya mun ji cewa fitaccen malami kuma shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Shiekh Ibrahim Khalil, ya shiga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Alamu sun nuna Tinubu ya fi karbuwa a yankunan Arewa, inji majiya

Shugaban ADC reshen jihar Kano, Musa Shuaibu Ungogo, shi ne ya tabbatar haka ga manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa Malamin tare da wasu manyan Farfesoshin Ilimi da ba'a faɗi bayanan su ba guda 8, sun zama cikakkun mambobin jam'iyyar ADC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel