Ministan Tinubu Ya Bayyana Mugun Mawuyacin Hali da Za a Shiga Idan Ba a Cire Tallafi Ba

Ministan Tinubu Ya Bayyana Mugun Mawuyacin Hali da Za a Shiga Idan Ba a Cire Tallafi Ba

  • Yajin da ake ci gaba da shan wahala bayan cire tallafin mai a Najeriya, Ministan Tinubu ya kare matakin da shugaban ya dauka
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu a Abuja
  • Minstan ya ce da ba a cire tallafin mai din ba da a yanzu haka ba a san halin da kasar ke ciki ba na mawuyacin hali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris ya kare matakin cire tallafin mai a kasar.

Minstan ya ce da ba a cire tallafin mai din ba da a yanzu haka ba a san halin da kasar ke ciki ba na mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

A kara hakuri: Minista ya ce ana daf da cin moriyar kudurorin Shugaba Tinubu a Najeriya

Ministan Tinubu ya bayyana halin da za a shiga idan akwai tallafin mai
Minstan Idris Ya Bayyana Mugun Mawuyacin Hali da Za a Shiga Idan Akwai Tallafi. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Mene Ministan ke cewa kan tallafin mai?

Idris ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed ya ce dole ne Tinubu da mukarrabansa suka sake sauya akalar kasar musamman ta fannin tattalin arziki.

A cewarsa:

"Ya kamata 'yan Najeriya su gane cewa dole ta saka Tinubu da mukarrabansa suka sauya akalar kasar ta fannin tattalin arziki tun daga farko."

Babban dalilinsa na kare cire tallafin

Ya kara da cewa:

"Ku duba maganar tallafi dole sai ta tafi, dole ne kuma ya sani za a fuskanci wahalalun cire tallafin, tabbas.
"Ya san da wahalar da za a shiga amma dole ya cire saboda idan ba a cire ba wahalar za ta fi haka, idan ba haka ko ayyuka ba za a iya yi ba."

Kara karanta wannan

Bayan cire tallafin man fetur, Ministan Tinubu ya bukaci cire na wutar lantarki, ya fadi dalilai

Ministan ya ce dole ne a samar da kudade da aka samu ta bangaren don ayyukan ci gaban kasa, cewar Daily Trust.

An bukaci Tinubu ya cireka tallafin wutar lantarki

Kun ji cewa Ministan Makaman a Najeriya, Adebayo Adelabu ya shawarci cire tallafin wutar lantarki a Najeriya.

Ministan ya ce hakan zai rage yawan basukan da kamfanin ke bin gwamnatin wanda ke hana samar da wutar ingantacciya a kasar.

Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel