"Ya Hadu Sosai”: Matar Aure Ta Cika da Farin Ciki Yayin da Mijinta Ya Wanke Mata Kayanta a Bidiyo

"Ya Hadu Sosai”: Matar Aure Ta Cika da Farin Ciki Yayin da Mijinta Ya Wanke Mata Kayanta a Bidiyo

  • Wata mata 'yar Najeriya ta cika da murna bayan ganin mijinta mai bukata ta musamman yana hada kayanta domin wanke mata su
  • Matar wacce ta cika da farin ciki bata kyale mutumin haka kawai ba, tana ta kwararo masa wakokin yabo da jinjina yayin da take godiya da wannan taimako da ya yi mata
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun nuna sha'awarsu akan ma'auratan, da dama sun yaba wa mijin sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matar aure ta yada bidiyonta cikin farin ciki bayan ganin mijinta yana hada kayanta domin ya tayata wanke su.

A cikin bidiyon na TikTok, an gano mutumin dauke da murmushi yayin da matar tasa ta fara yi masa kirari kan abun da yake shirin yi mata.

Kara karanta wannan

"Ba na bukatar kowani irin namiji": Budurwa ta bazama neman mijin aure, ta fadi irin wanda take so

Mata ta jinjuinawa mijinta
“Ya Hadu Sosai”: Matar Aure Ta Cika da Farin Ciki Yayin da Mijinta Ya Wanke Mata Kayanta a Bidiyo Hoto: @madamoyinandfamily
Asali: TikTok

Ta jinjina masa tare da kiransa da sunaye masu dadi yayin da take biye da shi a baya da kuma daukarsa bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daya daga cikin dalilan da suka sa nake sonka," ta rubuta a bidiyon.

Ta shafinsa na @madamoyinandfamily, ma'auratan sun saki bidiyoyinsu, suna nunawa masoyansu yadda suke tafiyar da rayuwarsu a matsayin mata da miji.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu kan bidoyon

King Reignz y ace:

"Aaahhhhh. Sannan ga ni nan ban samu masoyiya ba? Kamar dai nine ban mayar da hankali ga rayuwata ba.”

iamkizzo ya ce:

"Kuma ya hadu sosai amma me yasa kike kiransa da mumu kwanu?"

Blessing ta ce:

"Maza ba su yi tsada ba, ni ce nake neman wanda ya hada komai."

TFC chop_link ta ce:

"Nutsuwar mutumin ya yi ma shaa Allah yana da nutsuwa sosai, ji dadinki don Allah."

Kara karanta wannan

Matashi da ya mallaki naira miliyan 30 ya samu karayar arziki, ya koma rokon N2k

STAR GIRL OF CAMEROON ta ce:

"Ma shaa Allah yana da kyau ♥️ idan yana bukatar mata ta biyu ki tura mun sako saboda na fada sonsa."

Budurwa ta bazama neman mijin aure

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata jarumar mata yar Najeriya ta ayyana aniyarta na neman abokin rayuwa a dandalin X.

Matashiyar mai suna Adeshola Omo-eledumare (@tope_akan a manhajar X), wacce ke cikin shekaru 30 da 'doriya ta bayyana cewa tana bukatar namiji mai alkibla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel