'Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 10 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Akwa Ibom

'Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 10 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Akwa Ibom

  • ‘Yan sanda sun yi nasarar kame wasu da ake zargin sun addabi wani yankin Akwa Ibom da barna
  • An naqalto yadda suke sace mutane a wasu kananan hukumomi, inda da kansu suka amsa laifukansa
  • Ba sabon abu bane a Najeriya a kama wadanda ke garkuwa da mutane, har yanzu hukunta su ne aiki

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Akwa Ibom - Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wasu mutane 10 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, tuni kuma suka amsa laifinsu a lokacin da suka sha titsiyen ‘yan sanda.

'Yan sanda sun kame kasurguman 'yan bindiga 10
An kama 'yan dadi bindiga 10 a Akwa Ibom | Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan ‘yan sanda, Olatoye Durosinmi, ya ce wadanda ake zargin 10 na daga cikin mutane 79 da aka kama da zargin aikata laifuka a watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama ‘yan ta’addan

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Uyo, Durosinmi ya bayyana cewa kama mutanen 10 na daya daga cikin manyan nasarorin da rundunar ta samu a cikin watan.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa ‘yan sandan sun kwato bindigogin AK-47 guda hudu daga hannun wadanda ake zargin da ke shirin tayar da hankula a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin da suka amsa cewa su ‘ya’yan kungiyar asiri ne ta Iceland.

Inda suke aikata barna a jihar

Hakazalika, suke yin fashi a kananan hukumomin Ekpene Ukim, Uruan, Ibesikpo da Nsit Atai.

Kusan dukkan jihohin Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro, musamman a ‘yan shekarun bayan da lamurra suka lalace, rahoton BusinessDay.

Gwamnati na jami’an tsaro sun sha bayyana alkawuran kawo karshen rashin tsaro, amma har yanzu abubuwan na kara lalacewa.

Kara karanta wannan

Yan sandan Katsina sun aika da dan bindiga barzahu yayin harin da suka kai Dandume

Kiristoci sun nemi sojoji su kare su

A wani labarin, shugabannin addinin Kirista a Kudancin Kaduna sun daura alhakin kare rayukan mutanensu akan sojojin Najeriya.

Sun kuma yi kira ga jami’an tsaron da su dage wajen tabbatar da ba a ci gaba da kashe Kiristoci mazauna yankin da ma kasa baki daya ba.

Shugabannin a karkashin kungiyarsu ta SCKLA sun kuma bukaci mazauna yankin da su yi watsi da tsohuwar gaba da tashin hankali da ke yankin tare da rungumar zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel