Wata sabuwa: Monguno ya zargi Abba Kyari da kawo cikas ga kwangilar sayen makamai

Wata sabuwa: Monguno ya zargi Abba Kyari da kawo cikas ga kwangilar sayen makamai

Wasu sabbin bayanai sun sake bayyana dangane da karakaina da ake samu tsakanin mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Babagana Munguno da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari.

Premium Times ta ruwaito wadannan sabbin bayanai sun bayyana ne a cikin wasu takardu da ta yi ido hudu dasu wanda suka nuna rikicin ya samo asali ne a kan wata gagwgwabar kwangilar sayen makamai daga kasar hadaddiyar daular larabawa, U.A.E don amfanin rundunar Yansandan Najeriya.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Dan jaridar dake da hannu cikin satar N2.5bn ya yanke jiki ya mutu

Wata sabuwa: Monguno ya zargi Abba Kyari da kawo cikas ga kwangilar sayen makamai
Monguno da Abba Kyari
Asali: Facebook

A cikin wata wasika da ya aika ma ministan dake kula da harkokin Yansanda da babban sufetan Yansandan Najeriya a ranar 9 ga watan Disamba, Monguno ya zargi Kyari da yin watsi da umarnin shugaban kasa Buhari game da kwangilar sayen makamai.

A cikin wasikar, Monguno ya bayyana abin da Kyari yake yi a matsayin kasada da rashin hankali, wanda yace zai iya kunyata Najeriya tare da bayyanata a matsayin kasa mara kan gado a idon kawarta kamar UAE wanda aka santa a kan jajircewa.

Da wannan ne NSA ya yi gargadin Kyari ya sha yi ma umarnin shugaban kasa karan tsaye, tare da bayar da nasa umarnin na kashin kai, musamman a harkar tsaro, duk da yake ba shi da wani iko a kundin tsarin mulkin Najeriya na yin haka.

Don haka yace baya ga shi kansa Monguno a matsayinsa na NSA, babu wani da ke da ikon daukan mataki a kan harkokin tsaro illa ministan tsaro.

Sai dai Monguno bai bayyana yanayin makaman da Najeriya ke kokarin sayowa ba, amma dai ya bayyana kamfanin International Golden Group a matsayin kamfanin da kasashen biyu suka amince ta zama dillaliya a harkar sayen makaman, tun a shekarar 2016.

Amma duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin fadar shugaban kasa game da tirka tirkar ta ci tura, sakamakon Malam Garba Shehu da Femi Adesina sun ki cewa uffan game da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng