Garkuwa da mutane: Jami’an tsaro sun yi ram da wasu masu cinikin bindigogi

Garkuwa da mutane: Jami’an tsaro sun yi ram da wasu masu cinikin bindigogi

- ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wani mai safarar makamai a Jihar Kebbi

- Wannan mutumi da aka cafke, ya amsa laifinsa da kansa a hannun jami’ai

- Bayan haka, ‘Yan Sanda sun yi ram da wanda ake zargi ya na satar mutane

Jaridar Sun ta fitar da rahoto cewa dakarun ‘yan sanda na reshen jihar Kebbi sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da laifin safarar makamai.

Haka zalika ‘yan sandan sun yi ram da wani wanda ake tuhuma da laifin garkuwa da mutane.

Jami’in hulda da jama’a da yada labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar wa ‘yan jarida wannan a jiya.

Da yake jawabi a ranar Litinin, DSP Nafi’u Abubakar ya ce za a kai wadanda aka kama zuwa kotu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare motar ɗaukar gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamaci

“A ranar 27 ga watan Junairu, 2021, yayin da su ke ran-gadi a hanyar Malando/Garin-Baka, ‘yan sandan da ke babban ofishin Birnin Yauri, sun kama wani Ibrahim Bulus, 25, mutumin Dirin Daji a karamar hukumar Sakaba, dauke da bindigogin gida uku da babbar bindiga daya, da kuma wata karamar bindiga kirar gida.”

“Da aka yi masa tambayoyi, bai iya bada amsa mai gamsar wa game da inda ya samu bindigogin ba, don haka aka yi ram da shi.” Inji Nafi’u Abubakar.

Jami’in tsaron ya ce wannan mutumi ya tona cewa wasu mutum biyu; Ayuba Bulus, 42, da Usman Musa, 40 ne su ka aike shi, kuma tuni duk an cafke su.

KU KARANTA: Sayen kwayoyi da makamai ya sa aka hana mu’amalar ‘Cryptocurrencies’

Garkuwa da mutane: Jami’an tsaro sun yi ram da wasu masu cinikin bindigogi
IGP Mohammed A. Adamu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Har ila yau, ‘yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 27 daga garin Kangiwa, jihar Kebbi, Salihu Liman, wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane.

DSP Abubakar a madadin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Adeleke Adeyunka-Bode, ya yi kira ga jama’a su cigaba da sa-ido, da ba jami’an tsaro hadin-kai.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da rikicin makiyaya, inda ya bayyana cewa neman lalama da miyagun 'yan bindiga ba magana ba ce.

Nasir El-Rufai ya ce luguden wuta kurum zai kawo zaman lafiya da masu addabar jihohin Arewa.

Gwamna El-Rufai ya soki sulhun da wasu su ke yi, ya ce Sheikh Ahmad Gumi abokinsa ne, amma ba ya tare da shi a kan yunkurin sulhu da ‘Yan bindiga da yake yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel