Bayan sake tuhumarsa da laifuka 32 maimakon 18, Kotu ta amice da bayar da belin Dasuki

Bayan sake tuhumarsa da laifuka 32 maimakon 18, Kotu ta amice da bayar da belin Dasuki

- Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki yana gab da shakar iskar gari

- A yau wata babbar kotu ta sake abayar da belinsa kamar yadda ta bayar a shekarar 2015

- Kuma a wannan karon hatta lauya gwamnati bai kalubalanci bayar da belin ba

Alkalin babbar kotun birnin tarayya Abuja Mai shari’a Hussein Baba-Yusuf ya amince da bayar da belin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Col. Mohammed Sambo Dasuki, wanda aka gurfanar da shi gabansa bisa tuhumarsa karkatar da akalar kudaden da aka ware domin siyan makamai.

Bayan sabunta tuhuma 32 maimakon 18, Kotu ta amice da sake bayar da belin Dasuki
Bayan sabunta tuhuma 32 maimakon 18, Kotu ta amice da sake bayar da belin Dasuki

A yau dai ana tuhumar Dasukin ne tare da Aminu Baba Kusa da kuma kamfanin Acacia Holdings Limited and Reliance Referral Hospital da laifuka har 32.

Sai dai kuma wadanda ake zargin sun musunta aikata laifukan 32.

Idan ban da cire sunan Salisu Shuaib da aka yi a cikin sabbin laifuka 32 da ake tuhumar su Dasukin da su, babu wani sauyi da laifukan da ake zarginsa da aikatawa tun a shekarar 2015.

Ba jimawa ne a kotun bayan an gabatar da sabbin laifukan da ake zargin Dasukin da aikatawa ne sai rokon neman beli ta sako kai ta hannun lauyansa Adeola Adedekpe, tunda a cewar lauyan tun shekarar 2015 yake zuwa Kotun shari’a kan zargin, kuma shi ma lauyan gwamnati Oluwaleke Atolagbe bai kalubalanci neman belin ba.

A don haka ne mai shari’a Hussein Baba Yusuf ya ce ai dama tuni tun a shekarar 2015 ya bayar da belinsa, don haka kawai bangaren masu karar (Gwamnati) sai su martaba hukuncin da yayi tun sanda aka fara kawo shi gaban kotun.

Bayan sabunta tuhuma 32 maimakon 18, Kotu ta amice da sake bayar da belin Dasuki
Bayan sabunta tuhuma 32 maimakon 18, Kotu ta amice da sake bayar da belin Dasuki

KU KARANTA: Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

Idan za’a iya tunawa dai jami’an tsaron farin kaya DSS sun sake damke Dasukin ne a gidan yari na Kuje dake Abuja jim kada bayan cika sharuddan belinsa.

Ya zuwa yanzu, Alkalin kotun mai shari’a Baba Yusuf ya sanya ranar 3 da kuma 5 na watan Yuli domin fara gudananr da shari’a akan sabbin laifukan da aka gabatar.

Ainihi dai gwamnatin tarayya ta gurfanar da wadanda take zargin ne su biyar bisa tuhumar laifuka 18 a gaban kotun da aka sake gurfanar da Dasukin a yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng