An Kama Shugaban ’Yan Bindigar da Ake Zargin Sun Farmaki Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

An Kama Shugaban ’Yan Bindigar da Ake Zargin Sun Farmaki Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

  • Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama Ibrahim Abdullahi (Mandi) wanda ake zargin ya jagoranci kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
  • Mandi, wanda 'yan sanda suka kama a hanyar shiga Kaduna daga Abuja ta sha-tale-talen Rido, an kwato bindiga kirar AK-47 guda 48 a wajensa
  • Mandi shi ne ya jagoranci yin garkuwa da kuma kashe wasu daga cikin daliban jami’ar Greenfield tare da addabar hanyar Abuja-Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kama wani Ibrahim Abdullahi (Mandi), wanda ake kyautata zaton shi ne ya kitsa harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

Rundunar 'yan sanda ta kama wanda ya kitsa harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
'Yan sanda sun kama Ibrahim Mandi, wanda ya shirya harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja-Kaduna. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda 48 yayin da ake tsare da shi bayan ci gaba da binciken da ake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama Mandi a hanyar Abuja-Kaduna

A cewar rahoton SaharaReporters, 'yan Adejobi ya jaddada yunkurin rundunar na gano wanda ya dauki nauyin Mandi da kuma wanda ya kawo makaman.

Mandi shi ne ya kitsa tare da jagorantar yin garkuwa da daliban jami’ar Greenfield da kuma mafi yawan sace-sacen da ake yi a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muyiwa Adejobi ya ce an kama Mandi ne a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ta hanyar sha-tale-talen Rido a karamar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta koka kan yadda Borno ke biyan 'yan fansho N4,000 a wata

An kama wani jagoran 'yan bindiga

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa na kasancewa shugaban 'yan bindigar da ke addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja, rahoton Channels TV.

Rundunar ta kuma bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wani fitaccen shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane wanda ya kitsa wani hari a watan Satumban 2023.

Rundunar ta ce shi ne ya kai harin cocin Katolika na Saint Raphael da ke Fadan Kamatan inda aka kona cocin tare da wani malamin addini a ciki.

'Yan bindiga sun sace Shamakin Sarki

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun sace Shamakin Sarkin Zazzau tare da sakin bidiyonsa yana rokon sarkin ya kai masu dauki.

A cikin bidiyon da 'yan bindigar suka saki, an ga Alhaji Buhari, wanda ya ce shi ne Shamakin Sarkin yana magiya da a taimaka masu inda ya ce sun haura 600 a hannun 'yan bindigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel