Yanda za’a magance cin hanci da rashawa
-Shugaban masu shari’an Najeriya Mahmud Mohammed, ya ba da hanya mafi inganci da za’a bi don magance cin hanci da rashawa a kasar Najeriya, a ranar 18 ga watan Yuli
-Mohammed ya ce baza’a iya kawo karshen cin hanci da rashawa ba, ba tare da nuna gaskiya, dacewa da kuma saurin aiwatar da adalci a kasar Najeriya ba
-Ya yi kira ga dukkan jam’iyyun da ke da hannu cikin laifuka da cin hanci da rashawa da su ba gwamnati hadin kai na hukunta masu laif, na shekara 2015
Shugaban masu shari’an Najeriya Mahmud Mohammed ya ba da hanyoyin da za’a bi domin magance cin hanci da rashawa a kasar.
Da yake jawabi a gurin taron bitan aiki na kasa da kasa a kan bangaren shari’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa, wanda akayi a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin 18 ga watan Yuli, Mohammed ya ce cin hanci da rashawa ne muhimman hakkokin tattalin arzikin Najeriya, ci gaba da kuma alherin kasa.
Mohammed ya ce: “Na isa nace baza’a iya magance cin hanci da rashawa ta sauki ba, ba tare da nuna gaskiya, cancanta, da kuma saurin aiwatar da adalci ba. Lallai wannan shine muhimman hakkoki kan ci gaban tattalin arzikin mu, ci gaba da kuma alherin kasa."
KU KARANTA KUMA: Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Ya bayyana cewa , masu shari’a zasu fi kowa taka rawar gani, gurin kawo karshen cin hanci da rashawa. Mohammed ya kuma yi kira ga dukkan jam’iyyun da suke da hannu cikin cin hanci da rashawa ko kuma wani laifuka da sub a gwamnati daman aikata yunkurinta na adalci ga masu aikata laifi, na shekara 2015, domin tabbatar da cewa ba’a samu jinkiri a kotu ba.
Tunda ya hau kujerar shugabanci, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar gwamnatin ta hanyar hukumar hana cin hanci da almindana sun kafa kotu daban-daban kan wasu manya a kasar Najeriya.
Cikin wadanan mutanen sun hada da, tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkan tsaro, Sambo Dasuki, tsohon shugaban jami’an tsaro Alex Badeh, tsohon ministan cikin gida Abba Moro, wani dan uwan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da sauransu.
Wadanan na fuskantar chaji daban-daban na laifuka kama daga, satar kudi, zamba, cin amana da kuma cin kudin kasa.
Asali: Legit.ng